Sabon shugaban EFCC ya shiga aiki, ya ce an fara karbo kudin cuwa-cuwar tallafin fetur
- Hukumar EFCC ta ce ta iya gano wasu daga cikin kudin tallafin fetur da aka sace
- Abdulrasheed Bawa ya ce Hukumar EFCC ta sha alwashin kai barayin gidan yari
- Kawo yanzu EFCC ta iya karbo N20bn daga cikin N70bn da aka gano an wawura
A ranar Laraba, 10 ga watan Maris, 2021, sabon shugaban hukumar EFCC ta kasa, Abdulrasheed Bawa, ya yi magana game da badakalar tallafin man fetur.
Abdulrasheed Bawa ya bayyana cewa sun gano satar kusan Naira biliyan 70 da aka yi ta karkashin tsarin gwamnatin tarayya na biyan tallafin mai.
Jaridar Vanguard ta ce Mista Abdulrasheed Bawa ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya yi hira da manema labarai a babban kotu da ke Ikeja, a jihar Legas.
“Mun gano badakalar kusan Naira biliyan 70 da aka tafka ta tsarin biyan tallafin mai.” Inji Bawa.
KU KARANTA: Kwastam ta yi kamen kayan miliyoyi a jihar Katsina
“Kawo yanzu, hukumar (EFCC) ta gano kusan Naira biliyan 20, daga biliyan 70, kuma mu na kokarin karbo sauran.” Bawa yake fada wa ‘yan jarida jiya.
Bawa ya koka kan yadda shari’ar zargin cin kudin tallafin ta ke tafiyar hawainiya, shugaban hukumar EFCC ya ce za su cigaba da neman gaskiya a kotu.
“Eh, mun damu da rashin saurin shari’ar zargin cin kudin tallafin man da mu ka kai kotu tun shekarar 2012, a lokacin da aka karkare bincike.” Inji Bawa.
“Akwai sharudan da ake bi wajen shari’a da wanda ake zargi da laifi, za mu cigaba da binsu.”
KU KARANTA: Najeriya za ta karbo bashi daga China domin aikin dogon jirgin kasa
Bawa yake cewa: “Ina cikin masu bada shaida a shari’ar da ake yi da kamfanin Nadabo Energy na tsawon shekaru biyar, mu na sa ran za mu yi nasarar daure shi.”
Sabon shugaban na EFCC ya ce su na kokari dare da rana domin yin ram da wani da ake zargi da cin kudin tallafi, da ya tsere daga kasar bayan an bada belinsa.
Majalisar Najeriya ta bayyana cewa ta gano kamfanin mai na kasa watau NNPC ya karkatar da N4tr a cikin shekaru 5, ana zargin an yi wannan ne kafin 2016.
Kwamitin da ke binciken asusun gwamnati a majalisar dattawa ta jefi kamfanin NNPC da kin dawo da kudin da aka samu daga mai zuwa cikin baitul-mali.
Amma NNPC ya fito ya kare kansa, ya fadi yadda aka kashe wannan kudi tsakanin 2010 da 2015.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng