Bidiyon sankama daloli: Ganduje ya bukaci sauya rantsuwa da shaidu a gaban kotu
- Shari'a tsakanin Gwamna Ganduje da Jafar Jafar ta dauka sabon salo a ranar Litinin
- Ganduje na bukatar hutun kotu domin sabunta ikirarinsa, rantsuwa da sauya wasu shaidu
- Ganduje ya maka mawallafin a gaban kotu sakamakon wani bidiyo da ya bazu na zargin rashawa
Karar bidiyon daloli tsakanin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da mawallafin jaridar Daily Nigerian, Jafar Jafar, a ranar Litinin ta dauka sabon salo.
Wanda yayi karar ya bukaci hutun kotu domin gyara karar da sauran ikirarin da yayi a gaban kotun.
Ganduje ya maka mawallafin da wasu a gaban wata babbar kotun jihar Kano inda yake bukatar a biya shi N4 biliyan na bacin suna sakamakon wani bidiyo da ya bazu.
KU KARANTA: Hotunan addu'a ta musamman da Sarkin Kano ya jagoranta yayin cika shekara 1 a karagar mulki
KU KARANTA: Rundunar soji tayi martani ga Gumi akan tsokacinsa kan sojoji Kiristoci
A lokacin da aka kira shari'ar a ranar Litinin a gaban mai shari'a Na-Mallam, lauyan Ganduje, Ibrahim Nasarawa, ya bukaci kotun da ta bashi hutu domin karo shaidu, sauya shaida da kuma sauya takardar rantsuwa wacce kotun ta amince da hakan.
Alkalin yayi watsi da suka ta farko da lauyan mawallafin, Sunday Opoola ya shigar wacce yace wannan kamar sauya masu bashi kariya ne amma alkalin yace karin masu bashi kariya ne.
Mai shari'a Na-Mallam ya dage sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Afirilun 2021.
Idan za mu tuna, bidiyon da aka baza wanda ya nuna gwamnan yana sankama daloli a aljihun babbar rigarsa wanda ake zargi daga 'yan kwangila ne a jihar ya janyo cece-kuce.
A wani labari na daban, mambobin kungiyar ma'aikatan majalisu ta Najeriya a ranar Talata sun yi zanga-zanga inda suka mamaye majalisar dattawa dake Abuja, Channels TV ta wallafa.
A yayin zanga-zangar, ma'aikatan sun yi barazanar cewa za su mamaye dukkan majalisun jihohin fadin kasar nan idan ba a biya musu bukatarsu ba.
Shugaban kungiyar, Mohammed Usman, wanda yayi jawabi a madadin 'yan kungiyar inda yace 'yan majalisar tarayya sun dauka matakin da ya dace wurin baiwa ma'ikatar shari'a 'yancinsu saboda walwalar mambobinsu na tattare da wannan 'yancin.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng