Majalisar wakilai ta ƙalubalanci sanatoci kan rashin duba ƙudirin da suka aike musu dashi

Majalisar wakilai ta ƙalubalanci sanatoci kan rashin duba ƙudirin da suka aike musu dashi

- Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ya zargi sanatoci akan ƙin maida hankali akan kudirin da suka tura musu

- Doguwa yace kwata-kwata sanatocin basa musu adalci idan suka tura musu kudirin da suka amince dashi

- Shugaban masu rinjayen ya yi kira ga majalisun biyu da su haɗa kai wajen yin aiki tare don ganin an cimma nasara

Majalisun tarayya biyu, majalisar wakilai da ta dattijai sunci karo da juna wajen duba kudirorin da wata majalisa ta amince dashi. Jaridar Punch ta ruwaito

A zaman majalisar na ranar Laraba, Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa ya bayyana cewa majalisar dattijai basa duba kudirin da majalisar wakilai ta aike musu dashi a kan lokaci.

KARANTA ANAN: Kura ta kai bango: Mataimakin Shugaban kasa na kokarin sasanta mummunar rigimar APC a Imo

Ado Doguwa ya yi wannan magana ne lokacin da yake karanta wasu ƙudirori da majalisar dattijai ta aike musu dashi a zaman majalisar.

Shugaban masu rinjayen majalisar ya kara da cewa a watan maris ɗin shekarar data gabata mun amince da ƙudirin dazai bawa kamfanoni da ɗai-ɗaikun mutane tallafi Saboda matsin tattalin arziƙin da cutar korona ta jawo mana.

A ranar laraba, Ado Doguwa ya bayyana cewa: "Akwai kudirori da yawa da muka amince dasu kuma muka tura ma sanatocin, amma har yanzu basu duba su ba kamar yadda doka ta tanada."

Majalisar wakilai ta ƙalubalanci sanatoci kan rashin duba ƙudirin da suka aike musu dashi
Majalisar wakilai ta ƙalubalanci sanatoci kan rashin duba ƙudirin da suka aike musu dashi Hoto: @NGRsenate
Source: Twitter

A cewar Doguwa: "Mun ɗauki lamarin aiki da sanatoci dagasken gaske. Shiyasa ma muke saurin duba kudirin da suka aike mana dashi, amma abun takaicin shine su ba haka suke mana ba."

KARANTA ANAN: ‘Yan bindiga sun shiga Zamfara da Nasarawa, sun kashe Basarake da wasu mutum 30

"Akwai ƙudirorin da muka amince dasu anan muka tura musu, Wanda suna can a kan teburin shugaban kwamiti ba tare da an duba su ba. Wannan abun damuwa ne matuƙa," inji Alhassan.

Ado Doguwa ya ƙara da cewa akwai buƙatar majalisun biyu suyi aiki kafaɗa da kafaɗa, kuma su dinga bama ayyukan junansu muhimmanci.

A wani labarin kuma Hukumar kwastam reshen jihar Katsina ta bayyana cewa tayi ram da kayayyaki da suka kai kimanin 79 miliyan a wata biyu

Kayayyakin da suka haɗa da buhunan shinkafa, jarkokin mai, motar hawa, motar ɗaukan kaya da sauransu

A cewar shugaban hukumar na jihar, kayayyakin zasu kai kimamin 79 miliyan, kuma an kama su ne daga watan Fabrairu zuwa Maris na wannan shekarar.

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwa nan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta na twitter @ahmadyusufMuha77

Source: Legit

Online view pixel