Kura ta kai bango: Mataimakin Shugaban kasa na kokarin sasanta mummunar rigimar APC a Imo
- Gwamnan Imo Hope Uzodinma da Sanata Rochas Okorocha ba a ko ga maciji
- Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo zai sasanta ‘Yan siyasar
- Jihar Imo na cikin inda rikicin cikin-gidan Jam’iyyar APC ya yi kamari sosai
Tsohon gwamnan Imo Rochas Okorocha, ya ce bai son rigimarsa da gwamna mai-ci Hope Uzodimma ta kai ga jawo tashin-tashina a jihar.
Jaridar The Cable ta rahoto Sanata Rochas Okorocha ya na wannan magana bayan ya gana da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.
Okorocha ya yi magana da ‘yan jarida a ranar Laraba, ya ce ba zai so rikicinsa da gwamnan Imo ya kara kamari bayan karbe masa wasu kadarori ba.
‘Dan siyasar ya wanke kan shi daga zargin da Uzodinma yake yi masa, ya ce bita-da-kulli ne.
KU KARANTA: Ana bukatar ‘Yan siyasan kirki su hada-kai a APC da PDP a kawo gyara - Rochas
Rochas Okorocha wanda yanzu Sanata ne ya ce: “Tambayar a nan ita ce ‘wani laifin Rochas ya yi?’ Na yi wani laifi da na kawo APC Kudu maso gabas?
“Lokacin da na kafa APC duk wadannan mutane ba su nan. Dukkansu su na jam’iyyar PDP.”
Ya ce: “Na yi ba daidai ba ne da na ba dangi na kwarin gwiwar su yi amfani da dukiyarsu wajen kawo wa jihar Imo cigaba, maimakon su tafi kasar waje.”
Okorocha ya ce makarantun East High College, Rochas Foundation College, da the Royal Spring Palm Hotel da aka rufe, duk na gidauniyar Rochas Fondation ne.
KU KARANTA: Za mu yi wa Gwamna Uzodinma hankali a Imo inji Hadimin Okorocha
“Me kake so ka cin ma? Yanzu da ka kama shi, ko ka sa aka tsare shi a kurkuku tare da ‘yan iskan-gari, nasarar me ka yi? Menene laifinsa? Babu komai!”
A halin yanzu ta kai cewa mai girma mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya na kokarin yin sulhu tsakanin Rochas Okorocha da Hope Uzodimma.
Majalisar dokokin jihar Ekiti ta ce za ta mara wa Gwamna Kayode Fayemi baya ya yi takarar Shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2023 saboda ya yi an gani.
Hakan na zuwa ne bayan wata kungiya ta ce ta samu wasu Sarakuna da manyan Yarbawa da ke goyon bayan gwamnan na Ekiti ya nemi kujerar shugaban kasa.
‘Yan majalisar na jihar Ekiti sun yi wa gwamnan mubaya’a, su ka kamanta shi da Obafemi Awolowo.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng