‘Yan bindiga sun shiga Zamfara da Nasarawa, sun kashe Basarake da wasu mutum 30

‘Yan bindiga sun shiga Zamfara da Nasarawa, sun kashe Basarake da wasu mutum 30

- ‘Yan bindiga sun hallaka mutane kimanin 16 a Osewu, jihar Nasarawa

- Wadanan miyagu sun dura karamar hukumar Toto dauke da makamai

- An kuma hallaka mutane da-dama a wani kauye a Muradun, Zamfara

Daily Trust ta fitar da rahoto cewa wasu ‘yan bindiga dadi sun shiga wani kauye da ake kira Osewu a karamar hukumar Toto, jihar Nasarawa, sun kashe mutane.

Daga cikin wadanda aka aika barzahu, har da Mai garin wannan kauye na Osewu, Abubakar Omazi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa bayan kisan Mai martaba Abubakar Omazi, ‘yan bindigan sun kashe wasu akalla mutane 16 a kauyen Osewu a safiyar Laraba.

Wani mazaunin wannan kauye da ya bada sunansa da Yahaya, ya ce ‘yan bindigan sun shigo ne da karfe 6:00, su ka kashe har da wani babban jagoran ‘yan sa-kai.

KU KARANTA: Ba zan taba yin sulhu da mugu ba - Gwamnan Kaduna

Mutanen kauyen sun gano wasu gawawwakin da su ke cikin jeji, kuma an birne wadanda aka kashen tun jiya kamar yadda addininsu na musuluncin ya yi tanadi.

Jaridar ta rahoto cewa shugaban karamar hukuma Toto, Alhaji Nuhu Dauda, da wasu jami’an tsaro sun ziyarci kauyen bayan wannan mummunan lamari ya auku.

A daidai wannan lokaci ne kuma aka samu labari cewa wasu ‘yan bindiga sun harbe mutane 13 a kauyen Damaga, a karamar hukumar Muradun da ke jihar Zamfara.

Wanda abin ya faru a gaban idonsa, ya ce wadannan mutane sun shigo kauyen ne a kan babura dauke da bindigogi, inda su ka shiga harbin mutane da rana-tsaka.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun ragargaji ƴan bindiga a jihar Katsina

‘Yan bindiga sun shiga kauyukan Zamfara da Nasarawa, sun kashe Basarake, mutum 30
Shugaban 'yan sandan Najeriya, M. A Adamu
Asali: Twitter

‘Yan bindigan sun shiga Damaga ne da kimanin karfe 1:00 na rana, a lokacin yara na makaranta.

A jiya ne aka ji cewa 'yan Operation Tura ta kai bango sun kashe Boko Haram, sannan sun raba su da bindigogansu da wasu manyan makamai da su ke barba da su.

A wata sanarwa da ta fito daga bakin rundunar, sojojin na Operation Tura Ta kai bango sun kai wa ‘yan ta’addan hari ne a yankunan Chikun Gudu da Kerenoa a Borno.

Dakarun sojojin kasa sun tattara miyagun makamai daga hannun ‘Yan Boko Haram a Marte.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng