'Yar minista da masu garkuwa suka sace da shaƙi iskar ƴanci bayan awanni 48
- Yan bindiga sun sako yar uwar ministan harkokin mata da suka sace a jihar Plateau
- An sace Dapit Karen ne a gidanta da ke Rantiya Lowcost tun a ranar Litinin 8 ga watan Maris
- Kakakin rundunar yan sandan jihar Plateau, Ubah Gabriel, ya tabbatar da sakin Karen
Dapit Karen, yar uwar ministar harkokin mata na kasa, Pauline Talen wacce masu garkuwa da mutane suka sace a safiyar ranar Litinin, ta kubuta daga hannunsu ta samu yanci.
An sace Karen ne a gidanta da ke Rantiya Lowcost a karamar hukumar Plateau ta Kudu a jihar ta Plateau, Daily Trust ta ruwaito.
DUBA WANNAN: Yanzun nan: 'Yan bindiga da kayan sojoji sun bude wa matafiya wuta a hanyar Benin-Ore
Idan mai karatu zai iya tunawa, a ranar Litinin, mun kawo rahoton yadda masu garkuwar suka nemi a biya su naira miliyan 5 a matsayin kudin fansa kafin su sako ta.
Wani daga cikin yan uwan wacce lamarin ya faru da ita, ya ce an sako ta ne bayan biyan fansar naira miliyan 2.5 bayan ta shafe kwanaki biyu a tsare.
Majiyar Legit.ng ta ce ba za ta iya tabbatar da wannan ikirarin ba.
KU KARANTA: Dama ta samu: An sake buɗe shafin bada tallafin rancen COVID-19 daga bankin CBN
Da aka tuntube shi, mai magana da yawun yan sandan jihar Plateau, Ubah Gabriel, ya tabbatar da sakin wacce aka yi garkuwar da ita amma bai ce komai ba game da biyan fansa.
Rahotanni sun ce a yanzu an kai wacce abin ya faru gidan wani kawunta da ake ganin za ta fi samun tsaro a can.
A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.
Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.
Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng