Yanzun nan: 'Yan bindiga da kayan sojoji sun bude wa matafiya wuta a hanyar Benin-Ore

Yanzun nan: 'Yan bindiga da kayan sojoji sun bude wa matafiya wuta a hanyar Benin-Ore

- Wasu yan bindiga sun kai wa matafiya hari a hanyar Benin-Ore a ranar Laraba 10 ga watan Maris

- Maharan sun halaka wasu mutane a cewar rahoton da wasu da abin ya faru a gabansu suka bada

- Tawagar rundunar yan sanda a jihar ta Ondo ta ce ta fara bincike a kan lamarin

Yan bindiga sun kai wa matafiya farmaki a babban titin Benin-Ore a safiyar ranar Laraba 10 ga watan Maris inda suka tada wa matafiyan hankula.

Duk da cewa a halin yanzu ba a san iyaka wadanda suka mutu ba, wani ganau da ya yi magana da manema labarai ya ce an kashe wasu matafiyan sakamakon harin, kamar yadda The News ta ruwaito.

Yanzun nan: 'Yan bindiga da kayan sojoji sun bude wa matafiya wuta a hanyar Benin-Ore
Yanzun nan: 'Yan bindiga da kayan sojoji sun bude wa matafiya wuta a hanyar Benin-Ore. Hoto: @FRSCNigeria
Source: Twitter

Yayin da wasu tafiya tilas ta saka suka ajiye motocinsu suka shiga cikin daji, wasu da suka yi yunkurin tserewa sun hadu da wasu gungun yan bindigan a wani daji da ke kusa da inda abin ya faru.

DUBA WANNAN: Dama ta samu: An sake buɗe shafin bada tallafin rancen COVID-19 daga bankin CBN

The Nation ta ruwaito cewa direbobin motocci daga bisani sun tare hanya don nuna rashin jin dadinsu game da yadda jami'an tsaro ba su kai wa abokan aikinsu dauki ba a harin da ya dauki kimanin awa daya da rabi.

An ce yan bindigan sun kai harin ne a wata mota Sienna mai lamba LSR 352GK kuma suka tsere a ciki bayan kammala fashin.

Direban Sienna da yan bindigan suka kwace suka yi fashi da ita ya yi magana duk da cewa ya nemi a boye sunansa, ya ce misalin karfe 2 na daren Laraba yan bindigan suka kwace motarsa bayan sun gama yi wa fasinjojin fashi.

KU KARANTA: Matawalle ya bawa ƴan bindiga wa'addin watanni biyu su tuba su miƙa makamansu

Ya kuma ce sun bindige direbobin bas su biyu; Francis Duru da Sunday Wahwa.

Tawagar yan sanda da ta yi magana da majiyar Legit.ng ta ce an fara bincike kan lamarin tare da bin sahun yan bindigan da bincika daji don nemo wadanda lamarin ya faru da su.

A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.

Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.

Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel