'Yan sandan Katsina sun ragargaji ƴan bindiga, sun aika ɗaya lahira, sun kwato AK-47
- Rundunar yan sandan Nigeria reshen jihar Katsina ta kashe dan bindiga ta kwato AK-47 dinsa
- Kakakin yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da afkuwar lamarin
- SP Isah ya ce lamarin ya faru ne a hanyar Runka-Baura na karamar hukumar jihar kafin a kai Illela
Dakarun yan sandan jihar Katsina, a ranar Talata a karamar hukumar Safana da ke jihar sun yi bata kashi da yan bindiga inda suka kashe daya suka kuma kwato bindiga AK-47, The Punch ta ruwaito.
An gano cewa lamarin ya faru ne a kan hanyar Runka-Baura na karamar hukumar jihar kafin a kai kauyen Illela.
DUBA WANNAN: Dama ta samu: An sake buɗe shafin bada tallafin rancen COVID-19 daga bankin CBN
Har ila yau, an gano cewa tawagar yan sanda ta Safana yayin sintiri a garin misalin karfe 12.30 na daren Litinin sun yi karo da tawagar yan bindiga biyar inda suka yi musayar wuta.
Kakakin yan sandan jihar, Gambo Isah ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Laraba cikin wata sanarwa.
Ya ce, a ranar Talata, 9/03/2021 misalin karfe 12.30 yan sandan Safana yayin sintiri a hanyar Runka-baure bayan an baro Garin Tambari kafin a kai Illela sun yi karo da yan bindiga biyar dauke da AK-47.
KU KARANTA: Matawalle ya bawa ƴan bindiga wa'addin watanni biyu su tuba su miƙa makamansu
"Tawagar yan sandan sun yi musayar wuta da su hakan ya yi sanadin kashe dan bindiga daya da kwace AK-47 dinsa da harsashin da ke cikinta. Ana gudanar da bincike."
A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.
Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.
Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng