Matawalle ya bawa ƴan bindiga wa'addin watanni biyu su tuba su miƙa makamansu

Matawalle ya bawa ƴan bindiga wa'addin watanni biyu su tuba su miƙa makamansu

- Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya bawa dukkan yan bindigan jiharsa wa'addin watanni biyu su tuba su mika makamansu

- Gwamnan ya ce muddin wa'addin watanni biyun ta cika, duk wani dan bindiga da ya yi saura zai fuskanci fushin hukuma

- Matawalle ya ce gwamnatin tarayya za ta aike wa jiharsa karin sojoji 6000 da za su taimaka wurin yaki da sauran yan bindigan

Gwamnan Bello Matwalle na jihar Zamfara ya bawa dukkan yan bindiga da ke jiharsa wa'addin watanni biyu su tuba su mika makamansu idan kuma ba haka ba su fuskanci fushin hukuma, rahoton The Punch.

Da ya ke yi wa manema labarai jawabi a gidan gwamnati a ranar Talata, Gwamna Bello Matawalle ya ce gwamnati za ta yi maganin duk wani dan bindiga da ya ki mika wuya kafin wa'adin ya cika.

Matawalle ya bawa ƴan bindiga wa'addin watanni biyu su tuba su miƙa makamansu
Matawalle ya bawa ƴan bindiga wa'addin watanni biyu su tuba su miƙa makamansu. Hoto: @MobilePunch
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Alƙali ya bada umurnin rataye mutumin da ya kashe mahaifinsa ya birne shi a masai

Ya kara da cewa nan ba da dadewa ba gwamnatin tarayya za ta aike da karrin sojoji 6000 zuwa jihar domin taimaka musu yaki da yan bindigan da suka yi saura.

"Na bak watanni biyu ku yi saranda ku mika makamanku sannan ku tuba kuma duk wani dan bindiga da bai rungumi zaman lafiya ba tabbas gwamnati za ta yi yaki da shi," in ji gwamnan.

KU KARANTA: Kotu ta raba aure saboda mata da yara suna lakaɗawa maigida duka

Ya yi kira ga dukkan kantomomin kananan hukumomi da masu rike da sarautun gargajiya su saka idanu a garuruwansu su kai rahoto idan an kai hari domin gwamnati ta dauki mataki.

A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.

Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.

Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel