Tirƙashi: Majilisar wakilai tace kuɗin da Burtaniya suka dawo dasu na jihar Delta ne

Tirƙashi: Majilisar wakilai tace kuɗin da Burtaniya suka dawo dasu na jihar Delta ne

- Majalisar wakilai sun tattauna akan kudirin da wasu ƴan majalissa daga jihar Delta suka kawo mata a kan kuɗin da Burtaniya ta dawo dasu

- Kuɗin dai an kwato su ne daga hannun tsohon gwamnan jihar Delta

- Majalisar ta dakatar da duk wani shiri na rabon kuɗin kuma ta naɗa kwamiti yayi bincike cikin sati biyu

Majalisar wakilan Najeriya ta tabbatar da kudi fam miliyan 3.4 da aka dawo dasu daga Burtaniya mallakar gwamnatin jihar Delta ne, Vanguard ta ruwaito.

Majalisar wakilan ta nemi gwamnatin tarayya ta hannun ministan kudi da ta dakatar da rabon kudin da aka kwato a hannun tsohon gwamnan Delta.

Majalisar ta cimma wannan matsayar ne bayan kudirin da yan majalisa guda tara karkashin jagorancin shugaban marasa rinjaye na majalisar, Hon. Ndudi Elumelu, a ya yin zamanta na ranar Laraba.

KARANTA ANAN: Hukumar Hisbah ta wanke jami'inta da aka yiwa zargin kai matar aure Otal, ashe 'yarsa ce

Majalisar kuma ta nemi ma'aikatar kudi da kuma ofishin ministan shari'a na kasa da su gabatar mata da dukkanin wasu takardu dangane da kudaden da aka dawo da su.

Masu goyon bayan kudirin sun hada da:

Ndudi Elumel; Hon. Victor Nwokolo; Hon. Nicholas Motu; Hon. Leo Ogor; Hon. Ossai Ossai; Hon. Julius Pondi; Hon. Ben Rollands Igbakpa; Hon. Hon. Efe Afe; Hon. Thomas Ereyitomi da Hon. Francis E. Waive.

Yayin da yake gabatar da kudin mai taken "Bukatar gaggawa ta dakatar da rabon kudaden da aka kwato daga hannun tsohon gwamnan jihar Delta"

Tirƙashi: Majilisar wakilai tace kuɗin da London zasu dawo dashi na jihar Delta ne
Tirƙashi: Majilisar wakilai tace kuɗin da London zasu dawo dashi na jihar Delta ne Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Mr Elumelu ya kafa hujja da cewa irin hakan ya taba faruwa inda aka mayar da kudaden sata ga jihohin Abia da Bayelsa.

KARANTA ANAN: Satar kudi: Tsohon Shugaban EFCC Magu, ‘CP Singham’, da Minista za su yi wa Maina shaida

Ya bayyana cewa:

"Kuɗin kimanin fam miliyan 4.3 na sata da aka kwato a hannun tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori, ana kan turasu asusun gwamnatin tarayya batare da neman hurumin gwamnatin Jihar Delta ko majalisa ba nan da sati biyu.

Kudaden da ake fadin an dawo da su mallakin mutanen jihar Delta ne saboda haka yakamata ace an dawo da su asusun jihar domin yin ayyukan cigaba," a cewarsa

Majalisar ta damu kan cewa idan aka bar gwamnatin tarayya tayi amfani da kudin ba tare da hurumin mutanen jihar Delta ba, za'a tauye musu hakkin su na cin moriyar albarkatun su.

Daga dukkan alamu da bayanai daga gwamnatin jihar Delta sun nuna hakikanin kudin yakai fam miliyan 6.2.

Sannan gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa fam miliyan 6.2 aka sanya ba fam miliyan 4.3 ba kamar yadda aka fada.

Majalisa tayi amanna cewa idan har gwamnatin tarayya ba ta daina taba kudaden ba, to tabbas kudaden da aka kwato zasuyi batan dabo.

Domin Amincewa da kudirin, majalisa ta umurci kwamitin kudi, sharia, basussuka da kuma kudaden da aka kwato daya binciki lamarin cikin sati biyu sannan ya dawo ma majalisar.

A wani labarin kuma Bayan tura dakaru 6000 Zamfara, Buhari ya baiwa 'yan bindiga wa'adin mika makamai

Shugaba Buhari ya baiwa 'yan bindiga wa'adin wata 2 su ajiye makamai a jihar Zamfara

Shugaban kasar ya kara da tura karin dakarun soji 6000 jihar domin murje 'yan ta'addan.

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwa nan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta na twitter @ahmadyusufMuha77

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262