Hukumar Hisbah ta wanke jami'inta da aka yiwa zargin kai matar aure Otal, ashe 'yarsa ce
- An sake jami'in Hisbah da aka yiwa kazafi ziyartar matar aure a Otal
- Hukumar yan sanda ta kammala bincike kuma ta tabbatar ba shi da laifi
- Jami'in ya shigar da wani gidan Rediyo kotu kan lamarin kuma ya nemi milyan 10
Hukumar Hisbah wacce ta shahara da tabbatar da bin koyarwan Musulunci ta wanke wani jami'inta, Sani Rimo, wanda aka yiwa zargin kai matar aure dakin otal.
An damke Rimo ne a makonnin baya bayan rahoton cewa an kamashi da matar aure a Otal.
Kamashi ya yadu a kafafen sada zumunta bayan labari a shirin "Inda Ranka" na tashar Freedom Radio.
Sahara Reporters ta ruwaito cewa jami'in hulda da jama'a na hukumar Hisbah, Nabahani Usman, ya ce an kammala bincike kan lamarin kuma an gano jami'in bashi da laifi ko kadan.
A cewarsa, matar auren da aka kamashi da ita diyarsa ce.
Ya ce matar ta samu wasu matsaloli ne da iyalan mijinta kuma aka ajiyeta a Otal kafin a yi sulhu tsakaninsu.
Sani Rimo ya je kai mata abinci ne a Otal din dake Sabon Gari inda mutane suka gansa kuma sukayi masa mumunan zargi.
DUBA NAN: Kyakkyawan Mulkin da Buhari ya yi ne zai ba APC nasara a Zaɓen 2023, Inji Akpabio
KU KARANTA: Zamu bai wa Kiristocin Arewa mafakar siyasa a Biafra, Nnamdi Kanu
Usman yace: "Halin da ake ciki shine bayan an kai lamarin wajen hukumar yan sanda, an kammala bincike kuma an tabbatar da cewa mutumin ba shi da laifin dukkan zargin da ake masa."
"Matar tamkar diya ce gareshi, ta samu matsala ne da iyalan mijinta kuma hakan ya sa suka ajiye ta a Otal zuwa lokacin da za'a yi sulhu."
"Basu bari iyayenta su san halin da take ciki ba amma mahaifinta ya samu labari kuma ya ke kai mata abinci Otal. Yayinda mutane suka ga jami'in Hisbah zai shiga Otal, sai suka fara ihun cewa jami'in ya je ganawa da matar aure a wajen, ba tare da sanin cewa diyarsa ce ba."
Yanzu mutumin ya shiga cikin wani irin hali kuma ya shigar da Freedom Radio kara. Sai sun biyashi milyan 10 kudin kazafi tare da bashi hakuri."
Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.
Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.
Asali: Legit.ng