Kyakkyawan Mulkin da Buhari ya yi ne zai ba APC nasara a Zaɓen 2023, Inji Akpabio
- Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai ƙaddamar da sabuwar hedkwatar Hukumar raya Niger Delta (NDDC)
- Ministan harkokin Niger Delta, Godswill Akpabio ya ce, kodan kyawawan ayyukan da Buhari keyi APC zata lashe zaɓe me zuwa
- Ministan ya yi kira ga gwamnonin PDP da su gudanar da zaɓen kananan hukumomi
Ministan harkokin Niger Delta, Senator Godswill Akpabio, ya ce kyakkyawan mulkin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ke gudanarwa zai ba jam'iyyar APC nasara a zaɓen shugaban ƙasa dake tafe.
Ministan yace ayyukan da shugaba Buhari keyi a kowane yanki na ƙasar nan zai ba jam'iyyar hamayya PDP matuƙar wahala suyi nasara akan jam'iyya mai mulki APC.
KARANTA ANAN: Matawalle ya bawa ƴan bindiga wa'addin watanni biyu su tuba su miƙa makamansu
Ministan ya yi wannan jawabi ne a sa'ilin da yake zantawa da manema labarai a kan shirye-shiryen da gwamnatin tarayya keyi na ƙaddamar da sabon Hedkwata na hukumar raya Niger Delta (NDDC).
A jawabin ministan yace:
"Jam'iyyar hamayya ta PDP najin tsoron ayyukan da gwamnatin Buhari keyi, saboda tasan zaiyi matuƙar wahala ta iya samun nasara a zaɓen shugaban ƙasan dake tafe."
KARANTA ANAN: Gwamnatin Buhari ta yi magana a game da rade-radin binciken Jigon APC, Bola Tinubu
Akpabio ya bayyana cewa a ranar Alhamis shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai ƙaddamar da sabuwar hedkwatar NDDC daga fadarsa. Dailytrust ta ruwaito
Ya kuma yi kira ga gwamnonin jam'iyyar hamayya ta PDP da su gudanar da zaɓukan kananan hukumomi a jihohin su.
"Da yawa daga cikin gwamnonin jam'iyyar PDP na amfani da kantomomi a kananan hukumomi don su gurɓata harkokin su," a cewar ministan.
Daga ƙarshe ya bayyana cewa wannan hedkwatar da za'a ƙaddamar, watsi akai da gininta na tsawon shekara 26 amma shugaba Buhari ya kammala ta.
A wani labarin kuma Dakarun sojin sama sun tsefe garuruwa 4 a Kaduna, sun hallaka ‘Yan bindiga barkatai
Rahotanni sun bayyana mana cewa dakarun sojojin Najeriya sun shiga kananan hukumomi hudu da ke jihar Kaduna; Birnin Gwari, Giwa, Igabi da kuma Chikun
Kwamishinan tsaron cikin gida na Kaduna, Samuel Aruwan ne ya bayyana wannan a wani jawabi.
Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwa nan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.
Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta na twitter @ahmadyusufMuha77
Asali: Legit.ng