Abubuwa 4 masu muhimmanci da ya kamata ka yi idan wani ya turo kudi asusun bankinka cikin kuskure

Abubuwa 4 masu muhimmanci da ya kamata ka yi idan wani ya turo kudi asusun bankinka cikin kuskure

- Matsaloli daga bangaren banki, ko kuma kuskure daga wajen mutum na iya sabbaba tura kudi asusun wani cikin kure

- Wani zubin kuma, za ka iya ganin shigowar kudi cikin asusun bankinka daga wanda ba ka tsammani

- Kwanakin baya wani mutumi da ya kashe irin wannan kudi ya tsinci kansa cikin Kurkuku

Kwanakin baya, hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikkin kasa zagon kasa watau EFCC ta gurfanar da wani mutumin da yaki mayar da kudi milyan biyu da aka tura asusun bankinsa cikin kuskure.

Wannan labari ya yadu ko ina a kasar inda mutane da dama suka bayyana ra'ayoyinsu.

Yayinda wasu ke cewa zasu kashe kudin duk da haka, wasu sun ce sun dau darasi kuma ba zasu kashe ba.

Hakan ya sa wani masanin harkokin kudi, Yinka Ogunnubi, ya yi kokarin ilmantar da jama'a yadda ya kamata su yi idan aka turo musu kudi cikin kuskure.

Yinka ya zayyana abubuwa hudu da ya kamata mutum yayi;

1. Ka sanar da bankinka a rubuce kuma ka tabbatar sun karbi wasikarka

2. Idan sun tabbatar kuskure ne, ka tabbatar da cewa an rubuta hakan tare da lambar asusun wanda yayi kuskuren

3. Idan mai kudin ya tuntubeka kuma ya bukaci ka dawo masa da kudinsa, kada kayi hakan, ka tuntubi bankinka a rubuce domin su tura masa.

4. An fi so ka bukaci bankin ta mayar masa da kanta maimakon kayi da kanka. Saboda ka wanke kanka daga lamarin gaba daya.

Ya kara da cewa: "Duk abinda dai za ka yi, kada ka taba kudin."

Abubuwa 4 masu muhimmanci da ya kamata ka yi idan wani ya turo kudi asusun bankinka cikin kuskure
Abubuwa 4 masu muhimmanci da ya kamata ka yi idan wani ya turo kudi asusun bankinka cikin kuskure Credit: @EFCC
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng