Sojojin Najeriya sun ragargaji yan Boko Haram, sun hallaka 25

Sojojin Najeriya sun ragargaji yan Boko Haram, sun hallaka 25

- Bayan kwato Marte, Sojoji sun lallasa yan ta'addan Boko Haram a Borno

- Wannan ya biyo bayan umurnin da shugaban hafsun sojin kasa, Ibrahim Attahiru yayi

- Wannan ya shiga jerin nasarorin da sabbin hafsoshin tsaron da Buhari ya nada suka samu

Sojojin Najeriya sun ragargaji yan ta'addan Boko Haram a artabun da sukayi a karamar hukumar Marte ta jihar Borno, Arewa maso gabashin Najeriya.

A cewar Hukumar, wannan artabu ya auku ne ranar Talata, 9 ga watan Maris, 2021.

Sojojin sun yi musayar wuta da ƴan ta’addan a farmakin da suka kai musu a garuruwan Kerenoa, Chikungudu da kewaye.

Mai magana da yawun hukumar, Mohammed Yerima yace sojojin sun samu nasarar kwace bindigogi kirar AK47 guda 20 da bindigogin 5FN biyar, 2 60mm Motar Tube da kuma motocin yaki biyu.

Yace: "Yayin sintiri, Sojojin sun yi arangama da ayarin yan ta'addan inda suka yi musayar wuta da su kuma suka hallaka su."

"A artabun, an hallaka yan ta'adda 25, yayinda aka kwato makamai irinsu: Browny Machine Gun 2, AK-47 guda 20, FN guda 5, 60mm Motar Tube biyu da motocin yaki 2."

"Sauran makaman da aka kwato sun hada da bindigar baro jirgin sama 3, roka 2, motocin yaki 2, da motar CJTF kirara Hilux 1, da sauransu."

KU KARANTA: Bidiyon sankama daloli: Ganduje ya bukaci sauya rantsuwa da shaidu a gaban kotu

Sojojin Najeriya sun ragargaji yan Boko Haram, sun hallaka 33
Sojojin Najeriya sun ragargaji yan Boko Haram, sun hallaka 33
Asali: UGC

DUBA NAN: Sarkin Zamfara: ‘Yan bindiga sun sace Ma’aikata fiye da 100 a makon da ya wuce ba a sani ba

A bangare guda, Sabon ƙwamishinan 'yan sanda da aka tura jihar Edo, Mr. Philip Ogbadu, ya yi ikirarin zai kuɓutar da duk mutumin da 'yan garkuwa da mutane suka sace a jihar cikin awanni huɗu kacal.

Kwamishinan ya kuma sha alwashin murƙushe duk wani ta'addanci a faɗin jihar.

Mr. Philip Ogbadu, ya faɗi haka ne a a babban birnin jihar Edo ranar talata, lokacin da yakai ziyara Sakatariyar ƙungiyar 'yan jaridu na jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel