Za'a fara yiwa mutan Kano allurar rigakafin cutar Korona

Za'a fara yiwa mutan Kano allurar rigakafin cutar Korona

- Jihar Kano ta shiga jerin jihohin da suke shirin fara yiwa al'ummarta allurar rigakafin Korona

- Sarkin Kano ya yi kira ga al'ummarsa su amince ayi musu wannan rigakafi

- Najeriya ta kaddamar da shirin bada allurar rigakafin Korona ranar Juma'a

Gwamnatin jihar Kano ta samu karban rigakafin AstraZeneca na cutar Korona 209,520, TheCable ta ruwaito.

Kwamishanan kiwon lafiya na jihar, Aminu Tsanyawa, ne ya karbi rigakafin ranar Talata a tashar jirgin Malam Aminu Kano madadin gwamnan jihar.

Tsanyawa ya ce gwamnatin jihar za ta fara mayar da hankali da jami'an kiwon lafiya wajen basu rigakafin kafin yiwa gamagarin jama'a.

Hakazalika ya ce gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, ya samu nasa.

Ya kara da cewa kwamitin yaki da cutar COVID-19 ta jihar za ta zauna domin shirya tsarin yadda za'a kaddamar da yiwa mutane allurar rigakafin.

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su amince da allurar ta Oxford-AstraZeneca ta Korona.

Ya yi kiran ne a fadarsa jim kadan bayan wani taron addu’a na musamman da aka gudanar domin tunawa da cikarsa shekara daya a kan karagar mulki.

DUBA NAN: Bidiyon sankama daloli: Ganduje ya bukaci sauya rantsuwa da shaidu a gaban kotu

Jihar Kano ta samu rigakafin Korona kimanin 210,000, za'a fara yiwa jama'a
Jihar Kano ta samu rigakafin Korona kimanin 210,000, za'a fara yiwa jama'a
Asali: UGC

KU DUBA: Sarkin Zamfara: ‘Yan bindiga sun sace Ma’aikata fiye da 100 a makon da ya wuce ba a sani ba

Jiya kun ji cewa Dapo Abiodun, gwamnan jihar Ogun, ya yi alurar rigakafin Korona na AstraZeneca - gwamna na farko a kasar da ya yi hakan.

Kwamishinan lafiya na jihar, Tomi Coker, ne ta yi wa Abiodun wannan allurar a ranar Talata, a Abeokuta.

Hakazalika, Gwamnatin tarayya ta ce allurar rigakafin da za'a yiwa 'yan Najeriya iri ɗaya ce da wanda akayima shugaban ƙasa manjo janar Muhammadu Buhari.

Shugaban hukumar lafiya, Dr. Faisal Shu'aib ne ya faɗi hakan yayin taron kwamitin yaƙi da cutar corona a Abuja.

Najeriya ta ƙaddamar da fara rigakafin a ranar Juma'a. Sannan a ranar Asabar aka tsirawa shugaban ƙasa da mataimakinsa rigakafin kuma annuna a kafar talabishin kai tsaye.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel