Mun baiwa 'yan bindiga buhu 7 na shinkafa don tseratar da rayukanmu, Jami'in kwastam
- Aliyu Mohammed, babban jami'in kwastam ya sanar da yadda suka baiwa 'yan bindiga buhu 7 na shinkafa
- Ya ce 'yan bindigan sun sace wasu jami'ansu ne a Katsina kuma suka bukaci buhu 7 ko kuma su kashe jami'an
- Mohammed ya koka da yadda jama'a ke kin goya musu baya, domin akwai lokacin da mutanen gari suka dinga jifansu
Aliyu Mohammed, shugaban sashi na 4 ta rundunar sintirin hadin guiwa a iyakokin kasar nan ta kwastam a arewa maso yamma, ya ce ya taba baiwa 'yan bindiga buhu bakwai na shinkafa domin samun 'yancinsa.
A yayin jawabi ga manema labarai a Katsina a ranar Talata, Mohammed ya ce lamarin ya auku ne a karamar hukumar Dutsinma ta jihar.
Mohammed yana tsokaci ne a kan kalubalen da jami'an hukumar kwastam ke fuskanta yayin sauke hakkin dake kansu, The Cable ta wallafa.
KU KARANTA: Hotuna: Hafsoshin tsaro sun dira jihar Zamfara, sun shiga ganawa da Matawalle
A yayin bada labarin karonsu da 'yan bindiga a dajin Katsina, yace 'yan bindigan sun bukaci buhu bakwai daga cikin buhuna 37 da muka kwace in har ana son a sako jami'ansu da rai.
Ya kara da yin bayanin cewa jami'ansu basu samun goyon baya cikakke daga jama'a.
Kamar yadda Mohammed yace, akwai wani lokaci da 'yan sumogal suka tara 'yan kauye da duwatsu suka dinga jifan jami'an kwastam.
KU KARANTA: Matashiya mai 'ya'ya 2 ta sheka lahira yayin da suke tsaka da lalata da saurayinta
A wani labari na daban, jihar Kano za ta karba kasonta na riga-kafin korona na AstraZeneca a ranar Talata. Tijjani Hussaini, shugaban kwamitin martani na jihar ya sanar da hakan a wata tattaunawa da aka yi dashi a gidan Talabijin na Channels a ranar Talata.
"Jihar Kano ta shirya karbar rigakafi. An sanar da NPHCDA cewa Kano za ta karba kasonta a yau. Mun yi tsammanin samunsa a jiya amma yau zamu samu aka ce," yace.
Ya ce jihar ta shirya kaso 70 na shirin fitar dashi tare da fara yi wa jama'a rigakafin bayan ta karba.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng