Hotunan addu'a ta musamman da Sarkin Kano ya jagoranta yayin cika shekara 1 a karagar mulki

Hotunan addu'a ta musamman da Sarkin Kano ya jagoranta yayin cika shekara 1 a karagar mulki

- Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya cika shekara daya kan karagar mulki

- Babban basaraken ya jagoranci addu'a ta musamman a yau Talata a babban masallacin Kano

- Ya kara da wallafa hotunan a shafinsa na Twitter inda aka yi wa sarkin addu'o'i na musamman

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya cika shekara daya a kan karagar mulkin dabo.

Domin tunawa da ranar da ya hau karagar mulkin, babban basaraken ya jagoranci addu'a ta musamman a babban masallacin jihar Kano.

Kamar yadda masarautar ta wallafa a shafinta na Twitter, "Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya jagoranci addu'ar cika shekara 1 a matsayin sarkin Kano a safiyar yau Talata, 9 ga watan Maris 2021.

"Allah ya taimaki Sarki, Allah ya ja zamanin sarki, ran sarki ya dade."

Hotunan addu'a ta musamman da Sarkin Kano ya jagoranta yayin cika shekara 1 a karagar mulki
Hotunan addu'a ta musamman da Sarkin Kano ya jagoranta yayin cika shekara 1 a karagar mulki. Hotodaga @HrhBayero
Source: Twitter

Hotunan addu'a ta musamman da Sarkin Kano ya jagoranta yayin cika shekara 1 a karagar mulki
Hotunan addu'a ta musamman da Sarkin Kano ya jagoranta yayin cika shekara 1 a karagar mulki. Hoto daga @HrhBayero

KU KARANTA: Matashiya mai 'ya'ya 2 ta sheka lahira yayin da suke tsaka da lalata da saurayinta

Hotunan addu'a ta musamman da Sarkin Kano ya jagoranta yayin cika shekara 1 a karagar mulki
Hotunan addu'a ta musamman da Sarkin Kano ya jagoranta yayin cika shekara 1 a karagar mulki. Hoto daga @HrhBayero
Source: Twitter

KU KARANTA: Hotuna da bidiyon gagarumin mai safarar miyagun kwayoyi, Bishi Taiwo, da NDLEA ta kama

A wani labari na daban, darakta janar na NADDC, Jelani Aliyu, ya kaddamar da sabon garejin gyaran ababen hawa na mata zalla a jihar Sokoto.

Rahotanni sun bayyana cewa garejin mai zaman kansa ne wanda NANA Girls and Women Empowerment Initiative suka kafa domin kafa tarihin gyaran ababen hawa ba ga maza ba kawai.

A yayin jawabi a taron, Aliyu ya taya sabbin kwararrun kanikawan mata murna inda ya bukaci su dage wurin aiki tukuru domin samun nasarori.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit.ng

Online view pixel