Ku Ƙara HaƘuri Da Makiyaya, Gwamna Yahaya Ga Gwamnonin Kudu

Ku Ƙara HaƘuri Da Makiyaya, Gwamna Yahaya Ga Gwamnonin Kudu

- Gwamnan Gombe, Muhammadu Yahaya, ya yi kira ga gwamnonin kudancin ƙasar nan da jam'ar su da su ƙara haƙuri da makiyayan dake yankinsu

- Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da yake ƙaddamar da allurar rigakafin wata cuta a Gadam, karamar hukumar Kwami

- Ya ce makiyaya na bin doka sauda kafa don haka yakamata abar su su rayu cikin aminci

Gwamna Muhammadu Yahaya na jihar Gombe ya kirayi daukacin gwamnonin kudu da kuma sauran al'ummar yankin da su yi haƙuri da makiyayan dake zaune a yankunansu.

Yahaya ya bayyana hakan ne ga ƴan jarida jim kaɗan bayan ƙaddamar da gangamin yin allurar rigafin wata cuta mai saurin yaɗuwa a cikin dabbobi.

Cutar mai suna CBPP, an ƙaddamar da rigakafinta a Gadam dake karamar hukumar Kwami. Punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Dama ta samu: An sake buɗe shafin bada tallafin rancen COVID-19 daga bankin CBN

Yace ba duka ayyukan laifuka da ake jingina ma fulani bane suke kasancewa sun aikata su.

Inda ya ƙara da cewa suna bin doka, saboda haka ya kamata abar su su rayu cikin aminci.

A jawabin gwamnan ya ce:

"Wannan wata matsala ce da mutane suke fuskanta, musamman ma makiyaya a jihohin kudu, inda ake jingina duk wasu ayyukan laifi garesu wanda ba dole ya kasance sune suka aikata ba."

Ku Ƙara HaƘuri Da Makiyaya, Gwamna Yahaya Ga Gwamnonin Kudu
Ku Ƙara HaƘuri Da Makiyaya, Gwamna Yahaya Ga Gwamnonin Kudu Hoto: @governorinuwa
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Bidiyon sankama daloli: Ganduje ya bukaci sauya rantsuwa da shaidu a gaban kotu

Ya ƙara da cewa: "Ina kira gare su da su cigaba da zama lafiya da kowa a duk inda suke."

"Ina kira ga gwamnonin kudu akan suyi haƙuri su cigaba da zama tare da makiyaya musamman ma wadanda suka kasance masu bin doka," inji gwamnan.

"Akwai buƙatar mu zauna lafiya a ko ina cikin ƙasar nan, don a samu cigaba, tattalin arziƙi ya haɓaka sannan rayuwar al'umma ta inganta." inji Yahaya.

A wani labarin kuma Ministan Buhari yace jam'iyyar APC zata ci zaɓen shugaban kasa mai zuwa saboda adalcin Buhari

Ministan yace ayyukan da shugaba Buhari keyi a kowane yanki na ƙasar nan zai ba jam'iyyar hamayya PDP matuƙar wahala suyi nasara akan jam'iyya mai mulki APC.

Ministan ya yi kira ga gwamnonin PDP da su gudanar da zaɓen kananan hukumomi

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwa nan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta na twitter @ahmadyusufMuha77

Asali: Legit.ng

Online view pixel