Gwamnatin Buhari ta yi magana a game da rade-radin binciken Jigon APC, Bola Tinubu

Gwamnatin Buhari ta yi magana a game da rade-radin binciken Jigon APC, Bola Tinubu

- Ministan shari’an Tarayya ya ce ofishinsa ba ya binciken Bola Tinubu

- Abubakar Malami ya ce amma watakila wasu hukumomi na binciken

- Malami ya ce ba zai iya magana a madadin hukumomin EFCC da CCB ba

Ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya watau AGF, ya ce babu binciken da yake yi a kan babban jigon jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu.

Abubakar Malami (SAN) ya yi wannan bayani a lokacin da aka gayyace shi zuwa shirin ‘Politics Today’ na gidan talabijin na Channels TV a ranar Talata.

Da aka yi hira da Abubakar Malami a ranar 9 ga watan Maris, 2021, ya ce ofishinsa bai da alaka da binciken Bola Tinubu, amma bai san sauran hukumomi ba.

Malami ya bayyana cewa ba zai iya cewa ko hukumar EFCC mai binciken masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta na binciken Tinubu ba.

KU KARANTA: Ana binciken Tinubu, EFCC ta na bin bayanan kadarorin da ya mallaka

Haka zalika Ministan bai da masaniya a game da gaskiyar jita-jitar da ake yi na cewa CCB mai binciken kadarori ta taso tsohon gwamnan na Legas a gaba.

Ministan shari’ar kasar ya ce wadannan hukumomi su na da damar da za su binciki duk wanda su ke zargi da laifi, kuma su gurfanar da shi a gaban kotu a Najeriya.

“Ofishin AGF kamar yadda ka sani, bai dauki wani mataki, ko ya shigar da wata kara a wani kotu a game da Bola Ahmed Tinubu ba.” Inji Abubakar Malami SAN.

Malami ya ce: “Amma a doka, ka san cewa EFCC da CCB, hukumomi da aka ba dama da cikakken iko su yi aiki, saboda haka ba zan iya ba ka amsa kai-tsaye ba.”

KU KARANTA: CAN ta taso Gwamna AbdulRazaqa a gaba, za ta kai shi kotu

Gwamnatin Buhari ta yi magana a game da rade-radin binciken Jigon APC, Bola Tinubu
Abubakar Malami SAN
Source: Twitter

AGF ya kammala: “Ofishin AGF da sashenta na shigar da korafi, ba ta fara shari’a ko bincike ta hanun wata hukuma, ko da EFCC ko CCB (a game da Tinubu ba)

Kwanakin baya, tsohon abokin tafiyar Muhammadu Buhari, kuma shugaban jam’iyyar CPC na farko, Rufai Hanga ya yi magana a kan 2023 da burin Bola Tinubu.

Sanata Rufai Hanga ya ce mulkin Najeriya zai yi wa Bola Tinubu wahala a 2023, ya ce gwamnonin APC sun daidaita shi da aka sauke Adams Oshiomhole daga mulki.

Tsohon shugaban na CPC ya bayyana cewa an kassara Tinubu a APC duk da wahalar da ya yi.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit Newspaper

Online view pixel