Dakarun sojin sama sun tsefe garuruwa 4 a Kaduna, sun hallaka ‘Yan bindiga barkatai

Dakarun sojin sama sun tsefe garuruwa 4 a Kaduna, sun hallaka ‘Yan bindiga barkatai

- Sojoji sun kai hare-hare a mafakar Miyagun ‘Yan bindiga a Jihar Kaduna

- An yi nasarar gano wasu ‘Yan bindiga da aka auka masu da jiragen sama

- Sojojin sun bi wadanda suka nemi su tsere, suka hallaka da-dama cikinsu

A wasu hare-haren sama da sojojin Najeriya su ka kai a karkashin shirin Operation Thunder Strike, OPTS, sun hallaka ‘yan bindiga da-dama a jihar Kaduna.

Rahotanni sun bayyana mana cewa dakarun sojojin Najeriya sun shiga kananan hukumomi hudu da ke jihar Kaduna; Birnin Gwari, Giwa, Igabi da kuma Chikun

Kwamishinan tsaron cikin gida na Kaduna, Samuel Aruwan ne ya bayyana wannan a wani jawabi.

Da yake magana a ranar 8 ga watan Maris, 2021, Mista Samuel Aruwan, ya bayyana cewa an ga ‘yan bindiga su na tsere wa da jiragen sama su ka kai masu hari.

KU KARANTA: Zan ba ‘Yan sintiri bindiga, su yi maganin 'Yan bindiga - Gwamna Bello

Ya ce: “An kashe ‘yan bindiga da-dama yayin da sojojin sama su ka kai hare-hare a wasu wurare a Birnin Gwari, Giwa, Igabi da kuma karamar hukumar Chikun.”

“An hangi ‘yan bindiga a wani wuri da ke kilomita shida yamma da Anaba, aka kai masu farmaki, bayan hare-haren, an kuma bi an lallasa wadanda su ka tsere.”

“Sauran wuraren da aka duba ba tare da an yi zargin akwai miyagu ba su ne: as Rikau, Galadimawa, Kidandan da Yadi, Polewire, Crossing Point, Gagafada, Manini, Udawa, sai titin Kaduna-Birnin Gwari da Ungwan Yako,”

“An laluba yankunan Anaba, Dogon Dawa, da Dan Sadau da kewaye, amma ba a ga motsin mutane ba.”

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun kashe 'yan ta'addan Boko Haram a Borno

Dakarun sojin sama sun tsefe garuruwa 4 a Kaduna, sun hallaka ‘Yan bindiga barkatai
Samuel Aruwan a taro
Asali: UGC

Kwamishinan ya ce a wani hari na uku, an kai wa dakarun Operation Taimako Yazo agaji.

“Bayan haka an duba kewayen Rahama, Albasu, Sabon Birni, Kutemeshi, Rikau, Galadimawa, Kaya, Fatika, Kidandan, Dogon Dawa, Kuduru, Damari, Takama, Maidaro.”

A jiya ne mu ka ji cewa wasu miyagun ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da ‘Yan mata uku ‘yan gida daya a Jihar Kogi. An sace matan ne a karamar hukumar Katon Karfe.

A tashin farko, ‘yan bindigan sun ce ‘yanuwan yaran sai sun biya fansar Naira miliyan 100. A halin yanzu ana tattauna wa da miyagun domin su rage wannan kudin.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel