Zan kuɓutar da duk wanda akai garkuwa dashi cikin awanni huɗu, inji sabon kwamishina
- Sabon kwamishinan 'yan sanda da aka tura jihar Edo ya lashi takobin yaƙi da duk wasu marasa son zaman lafiya a jihar
- Kwanishinan yace zai kuɓutar da duk wani da aka sace a jihar cikin a wanni huɗu
- Bazamu zauna mu zura ido kazo ka sace mutum kuma katafi dashi har na tsawon awanni huɗu ba, zamu zo mu kuɓutar dashi kuma mu kama ka, inji kwamishinan
Sabon ƙwamishinan 'yan sanda da aka tura jihar Edo, Mr. Philip Ogbadu, ya yi ikirarin zai kuɓutar da duk mutumin da 'yan garkuwa da mutane suka sace a jihar cikin awanni huɗu kacal.
Kwamishinan ya kuma sha alwashin murƙushe duk wani ta'addanci a faɗin jihar. PM News ta ruwaito
Mr. Philip Ogbadu, ya faɗi haka ne a a babban birnin jihar Edo ranar talata, lokacin da yakai ziyara Sakatariyar ƙungiyar 'yan jaridu na jihar.
KARANTA ANAN: Rundunar 'yan sanda ta sha alwashin magance satar mutane a jihar Ogun
Ya kuma ƙara da cewa, ba yadda za'ayi a sace wani mutum ya yi sati ba tare da an kuɓutar dashi ba.
Ogbadu ya ce an turoshi jihar ne don ya ƙarfafa tsaron jihar musamman ma yawaitar satar mutane da ake fama dashi.
A cewar sabon kwamishinan: "Babu yadda za'ayi ka sace mutum har na tsawon awanni huɗu, matukar ka ajiye shi na sama da wannan lokacin, to zamu kamo ka, kuma wannan shine aikin da muka sa a gaba."
"Bazai yuwu kazo hakanan ka ɗauke wani mutum ba sai kace kaza, idan muka kama ka da wannan aikin to ka shiga uku," inji sabon kwamishinan.
Kwamishinan bai tsaya anan ba inda ya cigaba da cewa:
"An faɗa mana wasu wurare da abun yafi ƙamari kamar hanyar Benin-Auchi, yankin ehor da kuma wasu yankuna, zamu sanya ido akan su kuma mukasance a shirye, koda wani abu ya faru, jami'an mu zasu yi gaggawar zuwa wajen."
KARANTA ANAN: Mun baiwa 'yan bindiga buhu 7 na shinkafa don tseratar da rayukanmu, Jami'in kwastam
CP Ogbadu, ya bayyana cewa, akwai wasu masu aikata waɗannan laifuffaka da ba 'yan jihar bane, daga wasu jihohi suke, to amma zamu haɗa kai da duk wanda yakamata don ganin an murkushe 'yan ta'adda.
A cewarsa: "Yadda mutanen ke ta'andancin su a dazuzzuka a wasu jihohin, ba zasu yi haka anan ba saboda muna aiki kafaɗa-da-kafaɗa da jami'an sa kai da kuma dukkan hukumomin tsaro."
Shugaban majalisar ƙungiyar ƴan jaridar, Sir Roland Osakue, wanda ya tarbi kwamishinan da jama'arsa ya tabbatar ma kwamishinan, yan jarida zasu bada haɗin kai ga rundunar 'yan sanda a duk faɗin jihar.
A wani labarin kuma Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya bawa yan bindiga watanni biyu su miƙa makamansu
Gwamnan ya ce muddin wa'addin watanni biyun ta cika, duk wani dan bindiga da ya yi saura zai fuskanci fushin hukuma
Ya kara da cewa nan ba da dadewa ba gwamnatin tarayya za ta aike da karrin sojoji 6000 zuwa jihar domin taimaka musu yaki da yan bindigan da suka yi saura.
Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwa nan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.
Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd
Asali: Legit.ng