Rundunar 'yan sanda ta sha alwashin magance satar mutane a jihar Ogun

Rundunar 'yan sanda ta sha alwashin magance satar mutane a jihar Ogun

- 'Yan sandan jihar Lagos sun sha alwashin magance matsalar satar mutane a wasu yankunan Jihar Ogun dake makwabtaka dasu

- Kwamishinan 'yan sandan jihar ne ya bayyana haka a Ikeja, babban birnin jihar Lagos

- kwamishinan ya kara da cewa zamu tattauna da masu ruwa da tsaki a yankunan da ke da iyaka da mu don ganin yadda za'a bullo ma lamarin

Rundunar 'yan sandan jihar Lagos ta bakin kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Hakeem Odumosu, ya ce suna ɗaukar matakai don ganin an magance sace-sacen mutane a wasu yankunan jihar Ogun.

Kwamishinan ya ce shirye-shirye sunyi nisa domin magance matsalolin satar mutane da kuma faɗace-faɗacen da ake samu tsakanin manoma da makiyaya a wasu yankunan jihar.

KARANTA ANAN: Rundunar 'yan sanda ta yi magana kan wasu mutane masu raƙuma da suka ɓulla a Kano

Kwamishinan yace: "Duk da cewa muma muna da namu matsalolin a gida kuma a yanzun haka muna sake duba tsarin tsaron jihar mu, hakan bazai hana mu yin wannan aikin ba."

Odumosu ya faɗi haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Ikeja babban birnin jihar Legas kafin fara taronsa da shuwagabannin yankuna da na gundumomi.

"Domin kare wasu yankunan jihar mu ta Legos da ke da iyaka da wasu ƙauyukan jihar Ogun, mun tuntuɓi masu ruwa da tsaki a kauyukan dake iyakar don ganin yadda zamu ɓullo ma lamarin." A cewarsa

Rundunar 'yan sanda tasha alwashin magance sace-sacen mutane a jihar Ogun
Rundunar 'yan sanda tasha alwashin magance sace-sacen mutane a jihar Ogun Hoto: @policeNG
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Za'a yiwa 'yan Najeriya allurar rigakafi iri ɗaya da na Buhari, Inji gwamnatin tarayya

A cewar Kwamishinan:

"Munyi taro a garin Ikorodu don tattauna lamarin tsaron mutanen dake iyakar mu da Ogun. Kuma wakilan kabilun yankin sun halarci taron, kuma an samu matsaya akan yadda za'a dawo da zaman lafiya a yankunan."

"Mun ɗauki matakai kamar yadda mukayi lokacin kullen cutar corona, mun saka shingaye a yankunan iyakar." The Nation ta ruwaito

"Bazamu bar wani abun hawa ya shigo jihar mu ba sai mun bincikeshi ," inji kwamishinan.

Odumosu yace suna fuskantar damina (rainy) ne nan gaba, don haka dole ne su ƙara dagewa, wanda dalilin hakan ne yasa kwamishinan ya tuntuɓi shugabannnin yan sanda na gundumomi domin su kasance a shirye.

A wani Labarin kuma Ministan Buhari da matarsa sun sabunta rijistar jam'iyyar APC a Rivers

Ministan sufuri Chibuike Amaechi Tare da me ɗakinsa Dame Judith Amaechi sun sabunta rijistar su da jam'iyyar APC a jihar Rivers.

Amaechi ya yabawa wakilan jam'iyya da ke kula da aikin din rijistar

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwa nan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta na twitter @ahmadyusumuha77

Asali: Legit.ng

Online view pixel