'Yan bindiga sun afkawa wani ƙauyen Kaduna, sun halaka mutum 3 sun raunata wasu

'Yan bindiga sun afkawa wani ƙauyen Kaduna, sun halaka mutum 3 sun raunata wasu

- 'Yan bindiga dauke da muggan makamai sun afka garin Ganji da ke karamar hukumar Igabi a Kaduna

- 'Yan bindigan da suka shiga garin a kan babur sun halaka mutane uku sannan sun raunata wasu guda biyar

- Wasu mazauna kauyen sun tabbatar da afkuwar harin an kuma yi kokarin jin karin bayani a bakin kakakin yan sanda amma hakan bai yi wu ba

'Yan bindiga sun kari kauyen Ganji da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna a yammacin ranar Talata inda suka kashe mutum uku suna raunta wasu biyar da harsashin bindiga.

Mazauna kauyen sun shaidawa Daily Trust cewa yan bindigan sun kai hari a Ganji, wani kauye da ke kusa da Albasu inda a bara yan bindiga akan babura suka kai hari suka kona gidaje da ababen hawa.

'Yan bindiga sun afkawa wani kauyen Kaduna, sun halaka mutum 3
'Yan bindiga sun afkawa wani kauyen Kaduna, sun halaka mutum 3. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kotu ta raba aure saboda mata da yara suna lakaɗawa maigida duka

Lado Ibrahim, mazaunan garin ya ce yan bindigan sun kai harin ne misalin karfe 5.30 na yamma a kan babura fiye da 30 mutum biyu a kowanne sannan suka harbi mazauna garin suka kuma bi ta kansu da babur.

Ya ce an kai mutum biyar zuwa asibiti sakamakon raunin harbin bindiga yayin da jirgin sojoji mai saukar ungulu ke shawagi a sararin samaniyar garin domin tsorata yan bindigan.

Wani mazaunin garin, Hamza Shafiu ya ce harin na Ganji ba zai rasa nasaba da sace wasu mutane daga kusa da garin ba a ranar Litinin da tserewar da daya daga cikin wadanda aka sace kuma dan garin Ganji ya yi.

KU KARANTA: Alƙali ya bada umurnin rataye mutumin da ya kashe mahaifinsa ya birne shi a masai

An yi kokarin ji ta bakin Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kaduna, ASP Mohammed Jalige amma wayar ba ta shiga sannan bai amsa sakon kar ta kwana da aka aike masa ba a zuwa lokacin hada wannan rahoton.

A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.

Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.

Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel