Alƙali ya bada umurnin rataye mutumin da ya kashe mahaifinsa ya birne shi a masai

Alƙali ya bada umurnin rataye mutumin da ya kashe mahaifinsa ya birne shi a masai

- Kotu ta samu wani matum mai shekaru 31, da laifin kashe mahaifinsa a Akwa Ibom

- Alƙalin kotun don haka ya yanke wa Edidiong hukuncin kisa ta hanyar rataya

- Edidiong ya zarge mahaifinsa da maita ne kuma da kashe jikokinsa inda hakan tasa ya kashe shi ya birne a masai

Wata babban kotun jihar Akwa Ibom da ke zamanta a ƙaramar hukumar Ikot Ekpene ta yanke wa wani mutum mai shekaru 31 hukuncin kisa ta hanyar rataya, The Punch ta ruwaito.

An samu Edidiong, ɗan asalin Ikot-Akara a ƙaramar hukumar Obot Akara da laifin kashe mahaifinsa, Mr Pius Ototi, wanda ya yi zargin maye ne.

Kotu ta bada umurnin rataye mutumin da ya kashe mahaifinsa ya birne shi a masai
Kotu ta bada umurnin rataye mutumin da ya kashe mahaifinsa ya birne shi a masai. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta yi magana kan wasu mutane masu raƙuma da suka ɓulla a Kano

A yayin amsa tambayoyin ƴan sanda, Edidiong ya amsa cewa ya halaka mahaifinsa ya birne shi cikin masai a ranar 18 ga watan Nuwamban 2018.

Da ya ke yanke hukunci a ranar Litinin, Mai Shari'a Augustine Odokwo ya ce wanda ake zargin ya aikata "kissar gilla wadda ta ci karo da sashi na 326(1) na criminal code na dokokin jihar Akwa Ibom, shekarar 2000 kuma hukuncinsa kisa ne."

Mai Shari'a Odokwo ya bada umurnin a rataye Odokwo ta wuyarsa har sai ya ce ga garinku.

Ya ce tawagar masu shigar da ƙara da ma'aikatar Shari'a na jihar sun gamsar da kotu cewa ya aikata laifin.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC ba ta tausayin ƴan Nigeria, in ji Sule Lamido

Ya kara da cewa wanda aka yanke wa laifin ba shi da ikon ɗaukan ran mahaifinsa mai shekaru 60 da ya ke zargin dalilinsa ne jikokinsa suka mutu da ƙuruciya.

Wanda aka yanke wa hukuncin ya ta karanto ayoyin Bible yana roƙon Alƙali ya yafe masa ya yi masa afuwa.

A wani rahoton daban kunji cewa kungiyar musulmi ta Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta ce ba za ta hallarci mukabala da gwamnarin jihar Kano ta shirya da Sheikh Abduljabbar Kabara ba, Daily Trust ta ruwaito.

An shirya yin mukabalar ne a ranar 7 ga watan Marisa tsakanin malaman Kano da Sheikh Abduljabbar da ake zargi yana yi wa Annabi Muhammad batanci cikin karatunsa.

JNI, da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ke shugabanta, ta ce bata da masaniya kan matakan da aka dauka kawo yanzu don warware rashin fahimtar

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel