Gobara ta kone dangi mutum 4 kurmus a Bida dake jihar Neja

Gobara ta kone dangi mutum 4 kurmus a Bida dake jihar Neja

- Wata gobara ta cinye ahali guda kurmus kuma bata bar komai a gidan da abin ya shafa ba

- Rahotanni sun ce, gidan ya kone da wasu mata manya biyu da jikokinsu dake rayuwa a gidan

- Etsu Nupe ya nuna jimami tare da aike da ta'aziyya ga iyalan wadanda abin ya rutsa dasu

An ruwaito cewa mutum hudu daga gida daya sun kone kurmus a wata gobara da ta tashi a Bida, jihar Neja, Daily Trust ta ruwaito.

An bayyana wadanda lamarin ya rutsa da su a matsayin mata da jikokin maigidan da ya konen.

An bayyana sunayen matan da Hajiya Salamatu da kuma Hajiya Jummai Kabaraini yayin da sunayen jikokin mai gidan kuwa sune Hauwa da Khairatu Mahmud kabaraini.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Litinin.

KU KARANTA: Rundunar sojojin Najeriya ba ta fahimci kalamaina ba ne, in ji Sheikh Gumi

Gobara ta kone dangi mutum 4 kurmus a Bida dake jihar Neja
Gobara ta kone dangi mutum 4 kurmus a Bida dake jihar Neja Hoto: The Nation
Asali: Twitter

Baya ga asarar rayuka, duk wasu abubuwa masu kima da suka hada da masu motsi da wadanda ba za a iya motsi wutar ta lalata su gaba daya.

Maigidan, wanda aka ce shi dan asalin garin Bida ne, Ahmadu Kabaraini ya rasu a baya. wakilin gidan a yanzu, Sallau Kabaraini, ya ce ba a iya gano musabbabin gobarar ba.

Etsu Nupe, shugaban majalisar sarakunan gargajiya na jihar, Alhaji Yahaya Abubakar, ya aike da sakon ta'aziyya ga dangin da abin ya shafa.

Etsu Nupe wanda wakilin Mayakin Nupe ya wakilta, Alhaji Yahaya Aliyu Mayaki, ya yi kira ga ’yan uwa da su ga abin da ya faru a matsayin qaddara daga Allah.

Babban limamin Bida, Sheik Adamu Yakatun, shi ya jagoranci sallar jana’izar.

KU KARANTA: Kwadago zata fara zanga-zangar baji-ba-gani kan batun mafi karancin albashi

A wani labarin, Wasu daliban Jami’ar Fasaha ta Tarayya dake Owerri (FUTO) biyu sun mutu bayan shakar hayakin janareta, Daily Trust ta ruwaito.

An tattaro cewa daliban sun kunna janareta tare da fuskanto da hayakinsa zuwa tagogin dakin da suke kwana.

Kakakin rundunar 'yan sandar Jihar Imo, SP Orlando Ikeokwu, a wata sanarwa, ya ce rundunar ta samu rahoton faruwar lamarin ne daga makwabtan daliban a Eziobodo, a yankin Ihiagwa dake Owerri ta yamma.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.