Matasa sun cinna ma ofishin 'yan sanda wuta a Imo, Mutum ɗaya ya sheƙa barzahu

Matasa sun cinna ma ofishin 'yan sanda wuta a Imo, Mutum ɗaya ya sheƙa barzahu

- Wani gungun fusatattun matasa sun cinna ma Ofishin 'yan sanda wuta a jihar Imo

- Mai magana da yawun 'yan sandan jihar ta Imo ya tabbatar da faruwar lamarin amma yace matasan ne suka fara farmakar 'yan sandan.

- Matasan sun cinna ma ofishin wuta ne don martani a kan kisan da wani ɗan sanda ya yiwa ɗan uwansu

Tsoro ya mamaye jihar Imo a safiyar yau Talata lokacin da wasu gungun matasa suka cika ofishin 'yan sandan ƙaramar hukumar Ihitte/Uboma wanda yake a garin Ishinweke.

Matasan sun cinna ma ofishin 'yan sandan wuta don nuna fushin su akan aika aikar da wani ɗan sanda ya musu.

KARANTA ANAN: Mun shirya tsaf don karbar ragamar mulkin Najeriya a zaben 2023, jam'iyyar PDP

Wakilin jaridar Punch ya gano cewa matasan sunyi wannan ɓarnar ne don martani bisa kashe wani matashi da ɗan sanda yayi a yankin su.

Rahoton ya bayyana cewa jami'an 'yan sanda biyu sunji rauni sanadiyyar faruwar lamarin.

Da aka tuntuɓi mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Orlando Ikeokwu, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Matasa sun cinna wa ofishin 'yan sanda wuta a Imo, Mutum ɗaya ya sheƙa barzahu
Matasa sun cinna wa ofishin 'yan sanda wuta a Imo, Mutum ɗaya ya sheƙa barzahu Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Ikeokwu, yace jami'an yan sanda sun je yankin ne domin su kama wani mai laifi amma sai matasan suka farmake su.

KARANTA ANAN: Yanzun nan: Gwamna Dapo Abiodun ya zama gwamna na farko da ya fara yin rigakafin Korona

Matasan sun jikkata jami'an yan sanda biyu kuma suka saki mai laifin da jami'an suka kamo.

Sai dai tsautsayi yasa wani harsashi ya sami ɗaya daga cikin matasan wanda daga baya ya sheka barzahu bayan an garzaya da shi asibiti.

Mai magana da yawun 'yan sandan, Ikeokwu, yace an tura jami'ai da yawa zuwa Ofishin 'yan sandan, ya kuma ƙara da cewa kwamishinan 'yan sandan jihar, Nasiru Muhammed, ya bada umarnin yin bincike a kan lamarin don gano musabbabin faruwar hakan.

A wani labarin daban kuma, Mahaifin ɗaya daga cikin ɗaliban Jangeɓe da aka kuɓutar dashi Yace Allah yasa ɗiyata ce zata zamo silar kuɓuta na daga hannun 'yan ta'adda.

Malam Iliya gwaram ya bayyana yadda ya haɗu da ɗiyarsa a wajen masu garkuwa da mutane.

Saidai mutumin yace dole tasa ya ce ma ƴarsa kada ta nuna tasanshi dan gudun wata matsalar ta daban.

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwa nan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262