Allah ya yi diyata za tayi sanadiyar kubuta na daga hannun yan bindiga, Mahaifin Daya Daga daliban Jangebe

Allah ya yi diyata za tayi sanadiyar kubuta na daga hannun yan bindiga, Mahaifin Daya Daga daliban Jangebe

- Malam Iliya gwaram ya bayyana yadda ya haɗu da ɗiyarsa a wajen masu garkuwa da mutane

- Dole tasa na cewa 'yata kada ta nuna ta sanni don gudun kada a samu matsala, inji Gwaram

- Mahaifin yarinyar ya bayyana yadda iyalan wasu mata biyu suka biya 2 miliyan amma masu garkuwan basu sake musu 'yan uwan su ba

Malam Iliya Gwaram, mahaifi ga ɗaya daga cikin ɗalibai mata da ɓarayi suka sace a Jangebe ya samu kuɓuta jiya litinin da daddare daga hannun masu garkuwa da mutane da suka yi garkuwa dashi.

jaridar PM ta ruwaito cewa, da misalin ƙarfe 9 na daren jiya ne dai malam Iliya ya samu isa gidan gwamnatin jihar Zamfara dake Gusau.

KARANTA ANAN: Za'a yiwa 'yan Najeriya allurar rigakafi iri ɗaya da na Buhari, Inji gwamnatin tarayya

Ya bayyana cewa ya faɗa ma ɗiyar shi cewa kar ta nuna ta gane shi a yayin da yayi kaciɓis da ita a wajen masu garkuwa.

Legit.ng ta samu bayanai cewa mutane tara ne aka kuɓutar. A cikin su akwai mata masu shayarwa da kuma ƙananan yara guda uku.

Yadda Mahaifin Daya Daga Cikin Daliban Da Aka Sace Ya Kuɓuta Daga Wajen Masu Garkuwa
Yadda Mahaifin Daya Daga Cikin Daliban Da Aka Sace Ya Kuɓuta Daga Wajen Masu Garkuwa Hoto: @dailytrust
Asali: Twitter

Mutumin yace:

"Na shafe tsawon watanni uku a hannun masu garkuwa da mutanen tare da waɗannan mutanen da aka kuɓutar damu. Kwatsam ranar wata juma'ah da safe sai naga an kawo waɗannan yara ɗalibai zuwa inda muke."

Yace yayi kukan da bai taɓa irin shi ba tunda yazo duniya a ranar da aka saki ɗaliban, sabili da ya ƙaddara cewa shikenan bazai ƙara ganin ɗiyar tashi ba har abada.

Sannan ya ƙara da cewar bai sani ba ko an biya kudi kafin a sake su ko kuma ba'a biya ba. Shidai babban burinsu kawai shine suga sun koma gidajen su.

KARANTA ANAN: Ni ma fa Soja ne kuma ina alfahari da hakan, amma akwai batagari cikinku, Gumi ya yiwa hukumar Soji raddi

Ya ƙara da cewa ƴan uwan matan guda biyu da aka kuɓutar dasu a tare sun biya 2 miliyan tun kusan watanni 2 da suka gabata, amma duk da haka ba'a sake su ba.

Barayin sun nuna cewa ba su aka kawo ma kudin ba, illa iyaka dai, wasu gungun masu garkuwar ne suka amshi kuɗin fansar daga gurin wanda aka aiko ya kawo kuɗin.

Iliya gwaram ɗin ya bayyana cewa lallai yarinyar shi zata cigaba da karatu, inda ya ce da yarinyar bata da ilmi to lallai data tona su a lokacin data ganshi wanda hakan kuma da ya jefa su cikin matsanancin hali.

Idan baku manta ba, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Zamfara ta sanya dokar hana fita garin na Jangebe dake Karamar hukumar Talata Mafara daga faɗuwar rana zuwa wayewar gari.

Sulaiman Anka, kwamishnan yaɗa labarai na jihar ne ya bayyana ma manema labarai hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

A wani Labarin kuma Ministan Buhari da matarsa sun sabunta rijistar jam'iyyar APC a Rivers

Ma'auratan sunje runfar zaɓen su mai lamba 14 dake karkashin karamar hukumar Iwerre Don sabunta katin su na zama yan APC

Amaechi ya yabawa wakilan jam'iyya da ke kula da aikin din rijistar

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwa nan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd

Asali: Legit.ng

Online view pixel