Mutum 10 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon hadarin mota a Bauchi

Mutum 10 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon hadarin mota a Bauchi

- Allah ya yi wa mutane 10 rasuwa sakamakon hatsarin mota da ya ritsa da su a Azare, Bauchi

- Hatsarin ya faru ne sakamakon gudu fiye da kima da direban bus din ke yi a cewar hukumar FRSC

- Wadanda lamarin ya shafa sun hada da maza 14, mata biyar karamin yaro daya da kananan yan mata biyu

Hukumar Kiyayye Haddura ta Kasa, FRSC a jihar Bauchi ta tabbatar da rasuwar mutane 10 da wasu 12 da suka samu rauni sakamakon hatsarin da wata motar fasinjoji na jihar Gombe ta yi da mai babur Azare, karamar hukumar Katagum.

Shugaban FRSC na jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, yayin sanarwa manema labarai hakan a karshen mako a Bauchi ya ce mutum hudu da ke kan babur din sun mutu da mutum shida cikin bas din da ke dauke da fasinjoji 18, rahoton Daily Trust.

DUBA WANNAN: IWD: Fadar shugaban ƙasa ta lissafa mata 50 da ke riƙe da madafan iko a gwamnatin Buhari

Mutum 10 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon hadarin mota a Bauchi
Mutum 10 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon hadarin mota a Bauchi. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

A cewarsa, yin gudu fiye da ka'ida ne ya yi sanadin hatsarin.

"Mai babur din ya gita ta gaban Hummer bus din wacce ke mugun gudu kuma ta bige shi. Jami'an mu na Azare sun garzaya wurin sun ceci wadanda abin ya shafa sun kai su asibiti inda likita ya tabbatar 10 sun mutu.

"Jimillar mutanen da hatsarin ya ritsa da su 22 ne."

Ya ce wadanda lamarin ya shafa sun hada da maza 14, mata biyar karamin yaro daya da kananan yan mata biyu.

KU KARANTA: Jerin sunaye: BUK ta fara karatun digiri a sabbin kwasa-kwasai 8

Abdullahi ya ce an kai wadanda suka rasu dajin ajiyar gawa na asibiti yayin da sauran suna sabon asibitin Jama'are.

Ya shawarci masu ababen hawa su rika taka-tsantsan yayin tuki don rage hatsarin da zai janyo asarar rayuka da dukiyoyi.

A wani rahoton daban kunji cewa kungiyar musulmi ta Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta ce ba za ta hallarci mukabala da gwamnarin jihar Kano ta shirya da Sheikh Abduljabbar Kabara ba, Daily Trust ta ruwaito.

An shirya yin mukabalar ne a ranar 7 ga watan Marisa tsakanin malaman Kano da Sheikh Abduljabbar da ake zargi yana yi wa Annabi Muhammad batanci cikin karatunsa.

JNI, da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ke shugabanta, ta ce bata da masaniya kan matakan da aka dauka kawo yanzu don warware rashin fahimtar

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel