Da duminsa: Gagararren makashin makiyayi, Iskilu Wakili ya shiga hannun hukuma a Oyo

Da duminsa: Gagararren makashin makiyayi, Iskilu Wakili ya shiga hannun hukuma a Oyo

- OPC ta cafke gagararren dan bindiga kuma mai garkuwa da mutane, Iskilu Wakili, a jihar Oyo

- Kamar yadda Gani Adams ya tabbatar, an damke shi a safiyar Lahadi a Igangan dake Ibarapa

- An gano cewa Iskilu Wakili ne ke shirya yadda za a yi garkuwa da mutanen yankin

Gagararren dan bindiga makiyayi da ke addabar yankin Ibarapaa da Oke- Ogun na jihar Oyo, Iskilu Wakili ya shiga hannun hukuma.

Jaridar The Nation ta gano cewa an damke shi a safiyar Lahadi a Igangan dake karamar hukumar Ibarapa ta arewa.

Ana zargin Wakili da zama gagararren dan bindigan da ke jagorantar kashe-kashe da sace mutane a yankunan.

OPC ne suka cafke wanda ake zargin da satar mutanen.

KU KARANTA: Fani-Kayode ga Gumi: Kada ka saka Najeriya cikin rikici mai wuyar karewa da tsokacinka

Da duminsa: Gagararren makashin makiyayi, Iskilu Wakili ya shiga hannun hukuma a Oyo
Da duminsa: Gagararren makashin makiyayi, Iskilu Wakili ya shiga hannun hukuma a Oyo. Hoto daga @Thenation
Source: Twitter

Kehinde Aderemi, mataimaki na musamman a fannin yada labarai ga Aare Ona kakanfo na kasar Yarabawa, Gani Adams Adams ya tabbatar da kamen.

Kungiyar Yarabawa ta Afenifere ta jinjinawa OPC a kan wannan cigaban.

KU KARANTA: Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana babban sirrinsa na haddar Al-Qur'ani

A wani labari na daban, tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya hada kai da gwamnoni, shugabanni tsaro da sauran masu ruwa da tsaki wurin shawo kan matsalar tsaron kasar nan.

Jonathan yayi wannan kiran ne yayin da ya jagoranci wasu wakilan siyasa daga Bayelsa zuwa ta'aziyya ga Gwamna Ifeanyi Okowa a gidan gwamnatin Asaba na jihar Delta a kan rasuwar mahaifin gwamnan.

Ya ce abun takaici ne yadda ake sace yaran makarantu da sauran 'yan Najeriya, Daily Trust ta wallafa.

"Ina da tabbacin idan gwamnoni da gwamnatin tarayya suka mayar da hankali, zamu iya shawo kan matsalar rashin tsaro a kasar nan.

“Matukar gwamnoni, shugaban kasa da dukkan hukumomin tsaro za su yi aiki tare, Najeriya za ta iya tsallake wannan mummunan kalubalen da take fuskanta," yace.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit.ng

Online view pixel