Babu abin da zai hana ‘Dan Arewa cigaba da mulki bayan Buhari inji babban Gwamnan APC, Bello

Babu abin da zai hana ‘Dan Arewa cigaba da mulki bayan Buhari inji babban Gwamnan APC, Bello

- Yahaya Bello ya ce idan Allah ya rubuta zai yi mulki, to sai ya rike Najeriya

- Gwamna na Jihar Kogi ya ce babu abin da zai hana Arewa cigaba da mulki

- Bello ya ce dokar Jam’iyyar APC ba ta san da kama-kama a shugabanci ba

A ranar Lahadi, 7 ga watan Maris, 2021, gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya sake tado da muhawarar yankin da ya dace ya karbi shugabanci a 2023.

Tun yanzu ana maganar wanane zai karbi mulki tsakanin yankin Arewa da Kudu a zabe mai zuwa.

Jaridar This Day ta rahoto Yahaya Bello ya na cewa babu inda aka yi wata yarjejeniya cewa akwai tsarin karba-karba a cikin dokokin jam’iyyar APC mai mulki.

Da aka tambayi Gwamna Bello ko zai yi takarar shugaban kasa a 2023, sai ya ce: “Nufin Ubangiji ne da har na zama gwamna yau, ka ji yanzu ina wa’adina na biyu.”

KU KARANTA: Osinbajo @ 64: Shugaban kasa Buhari ba ya da na sanin zaben Mataimakinsa

“Idan Ubangiji ya yi nufin zan zama shugaban kasar nan wata rana, to hakan za ayi.” Inji Bello.

Bello ya ce kofa a bude ta ke; “Babu kama-kama a jam’iyyarmu. A 2015, babu wannan tsari, ‘yan takara har da Rochas Okorocha sun nemi tikiti (a zaben gwani)."

Bello ya ce: “A 2019, ba a samu wadanda su ka iya tsaya wa takara da Muhammadu Buhari ba.”

Bello ya na hangen nasara idan ya fito, “Zan samu kuri’un da ba a taba samu a Najeriya ba da yardar Allah. Amma ba ta wannan ake ba; ina amfanin badi ba rai?”

A cewar gwamnan na jihar Kogi, babu abin da ya shafi kalubalen da Najeriya ta ke fuskanta a yau irinsu matsalar tsaro da sauransu da kuma yankin shugaban kasa.

KU KARANTA: Masu ci da rashin tsaro ba za su yi sha’awar samun zaman lafiya ba - Bantex

Babu abin da zai hana ‘Dan Arewa cigaba da mulki bayan Buhari inji babban Gwamnan APC, Bello
Gwamna Yahaya Bello Hoto: @GovernorBello
Asali: UGC

Alhaji Yahaya Bello ya zo da ra’ayin da ya saba wa manyan APC irinsu gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai da gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Haka zalika wannan shi ne ra’ayin Sanatocin Kano irinsu: Kabiru Gaya, Malam Ibrahim Shekarau, da Ministan ayyuka da gidaje na kasa, Raji Babatunde Fashola SAN.

Gwamnan jihar Kaduna ya ce akwai alkawarin cewa bayan Muhammadu Buhari ya kammala wa’adinsa, shugaban kasa na gaba da za ayi, zai fito ne daga kudu.

Wani gwamnan Arewa da yake goyon-bayan Kudu ta karbi mulki a 2023 shi ne Babagana Zulum.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel