Kudu ya kamata a baiwa shugaban kasa a 2023 - El-Rufai

Kudu ya kamata a baiwa shugaban kasa a 2023 - El-Rufai

Yayinda ake cigaba da tattaunawa kan wanda jamiyyar All Progressives Congress, APC za ta baiwa tikitin takarar kujerar shugaban kasa a shekarar 2023, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa kudu ya kamata mulki ya koma bayan wa’adin Buhari.

Duk da cewan gwamnan Kadunan bai bayyana wani sashen yankin kudu za’a baiwa mulkin ba, ya ce ba’a yi adalci ba idan Arewa ta rantse its zata cigaba da rike mulki bayan karewar mulkin Buhari a 2023.

El-Rufa’i, wanda ya jagoranci kwamitin garambawul na jam’iyyar ya ce duk da cewan kundin tsarin mulkin jam’iyyar bata tanadi raba dai-dai tsakanin kudu da Arewa ba, akwai kyakkyawar fahimta tsakaninsu cewa saboda adalci, a baiwa kudu dama.

Kudu ya kamata a baiwa shugaban kasa a 2023 - El-Rufai
Kudu ya kamata a baiwa shugaban kasa a 2023 - El-Rufai
Asali: Original

Gwamnan yace: “Gama-garin fahimta a faggen siyasar Najeriya shine ayi zagayen mulki tsakanin Kudu da Arewa. Ba a rubuce yake ba amma kowa ya fahimci haka.“

“A APC, da gan-gan muka ki rubuta zagayen kujerar shugaban kasa a kundin tsarin mulkinmu shiyasa a 2015, Rochas Okorocha daga kudu maso gabas yayi takara, Sam Nda Isaih yayi takara, Buhari, Kwankwaso da sauransu sukayi takara.“

“Amma a matsayinmu na kungiya, ya kamata gamayyar yan APC a Arewa mu zauna domin marawa mutum daya baya, musamman daga kudanci, saboda bayan shekaru takwas na Buhari, ban tunanin shugaban kasa ya cigaba da kasancewa a Arewa sai dai idan akwai wani dambarwa.“

“Amma muddin komai zai cigaba da tafiya daidai, zamu cika alkawarinmu.“

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel