Buhari ya aikawa Mataimakinsa 'Dan halal' Osinbajo jinjina a ranar da ya cika shekara 64

Buhari ya aikawa Mataimakinsa 'Dan halal' Osinbajo jinjina a ranar da ya cika shekara 64

- Muhammadu Buhari ya taya Farfesa Yemi Osinbajo murnar cika shekaru 64

- Shugaban kasar ya ce ya yi alfaharin daukar Osinbajo a matsayin Mataimaki

- Buhari ya ce Osinbajo mutum ne mai kishi, saukin hali, hakuri da sanin-aiki

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aika wa mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, sako na taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Mai girma shugaban kasa ya fitar da jawabi ne a jiya ta bakin mai magana da yawun bakinsa, Malam Garba Shehu, ya na yabon Farfesa Yemi Osinbajo.

Muhammadu Buhari yake cewa ya yi alfahari da ya dauko Farfesa Yemi Osinbajo a shekarar 2015.

A jawabin da shugaban kasar ya fitar, ya bayyana Yemi Osinbajo a matsayin ‘mataimakin da za a dogara da shi, wanda ya dage kwarai a bakin aikin na sa.”

KU KARANTA: Rochas Okorocha ya yi bikin Valentine tare da mai dakinsa

Har ila yau, Buhari ya ce “Osinbajo ya nuna cewa ya san aiki, sannan ya na sha’awar aikin na sa.”

Kamar yadda jawabin ya bayyana, Buhari ya ambaci wasu daga cikin halayen mataimakinsa kamar hakuri, sanin aiki, da kishin kasa, sannan ya yi masa addu’a.

Shugaban Najeriyar ya kuma kara da cewa: “Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ‘dan siyasa ne mai hakuri, wanda ya nuna basirarsa wajen gabatar da aikinsa.”

“Na yi alfahari da na dauko Osinbajo a matsayin abokin takara na, kuma ya yi mani bakin kokarinsa tun da mu ka fara aiki tare a shekarar 2015.” Inji Buhari.

KU KARANTA: Shawarar Ahmad Gumi ta yi wa ‘Yan bindiga afuwa ba ta dace ba - Bantex

Buhari ya aikawa Mataimakinsa Osinbajo ruwan jinjina a ranar da ya cika shekara 64
Yemi Osinbajo da iyalinsa Hoto: Instagram @Dolapoosinbajo
Asali: Instagram

“Mataimakin shugaban kasa mutum ne mai saukin-kai, wanda ya ke sa Najeriya kafin la’akari da komai.”

Muhammadu Buhari ya yi wa Farfesa Osinbajo fatan alheri a wannan sabuwar shekara da ya shiga, ya kuma roki Ubangiji ya dafa masa, ya jagoranci al’ummarsa.

A ranar Lahadi, Mataimakin shugaban kasar Najeriyan ya bayyana irin wahalar da ke cikin gina kasa.

Mataimakin shugaba Yemi Osinbajo ya na ganin yawan kabilu da addinai da ake da su ne su ke jawo wa kasar kalubale. Jaridar The Cable ce ta fitar da wannan rahoto.

Osinbajo ya yi kira ga 'yan kasa su yi hakuri da juna domin kawo cigaba a Najeriya. Farfesan ya yi wannan magana ne a wajen wani taro da jaridar Global Patriot ta shirya.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng