Rashin tsaro: Tsohon Mataimakin Gwamnan Kaduna ya yi magana, ba ya goyon bayan Dr. Gumi

Rashin tsaro: Tsohon Mataimakin Gwamnan Kaduna ya yi magana, ba ya goyon bayan Dr. Gumi

- Bernabas Bala Bantex ya ce akwai wasu da ke cin riba da matsalar rashin tsaro

- Hon. Bantex ya ce masu cin moriyar rashin tsaro ba za su bari a zauna lafiya ba

- Tsohon Mataimakin gwamnan Kadunan ba ya goyon bayan yin sulhu da Miyagu

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kaduna, Bernabas Bala Bantex, ya ce masu cin ribar rashin tsaro ba za su so a kawo karshen wannan lamarin ba.

Da yake magana da gidan talabijin na Channels Television a shirinsu na siyasa a jiya ‘Sunday Politics’, ya tattauna halin rashin tsaro da ake fuskanta.

Bernabas Bala Bantex ya bayyana cewa ba ya yin na’am da kiran da ake yi ko kokarin gwamnatocin jihohi ko tarayya na yi wa ‘yan bindiga afuwa.

Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya na kan gaba wajen wannan kira.

KU KARANTA: An je an kashe mutane, an tsere da dabbobi 100 a jihar Sokoto

Bala Bantex ya na ganin yadda wasu gama-gari su ke samun ta-cewa a game da abin da ya shafi tsaron al’umma ya nuna yadda gwamnatin kasar da gaza.

“Jawabin Gumi ya nuna abubuwa sun gaza domin idan ana ba gama-gari damar su rika magana irin haka, a madadin hukuma, alama ce ta cewa an gaza.”

“Ba daidai ba ne yin sulhu da mutanen da su ka rusa tattalin arzikin dubunnan ‘Yan Najeriya, wadanda su ka lalata rayuwar jama’a kuma su na cigaba da yi.”

Tsohon mataimakin gwamnan yake cewa: “Akwai wasu mutane da su ke cin moriyar wannan halin, ba za su bari a shawo kan lamarin nan da wuri ba.”

Rashin tsaro: Tsohon Mataimakin Gwamnan Kaduna ya yi magana, ba ya goyon bayan Dr. Gumi
Tsohon Mataimakin Gwamnan Kaduna, Bala Bantex Hoto: www.greetingsmedia.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Wasu matasan Ibo ta buƙaci a kama Sheikh Ahmad Gumi

A game da wa’adin da Muhammadu Buhari ya ba hafsoshin sojoji, Bantex ya ce ya na sa ran shugaban kasar zai ba sojoji kayan yakin da su ke bukata.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an yankewa wasu 'yan Najeriya biyu hukuncin kisa a Ghana.

Wata babbar kotu a Sekondi da ke kasar Ghana ta yankewa Samuel Udoetuk Wills da kuma John Orji hukuncin kisa bayan kamasu da laifin kisan wasu mata.

Alƙalin kotun da ya yi wannan shari'a ya ce waɗanda ake zargi na da damar ƙalubalantar hukuncin a cikin kwanaki 30, ko a zartar masu da hukuncin.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng