A shekara ɗaya, Mun tara miliyan 400 saboda canza ranar haihuwa, JAMB

A shekara ɗaya, Mun tara miliyan 400 saboda canza ranar haihuwa, JAMB

- JAMB ta bayyanar da cewa a cikin shekara ɗaya tal, sun tara kuɗaɗe kimanin 400 miliyan saboda yawan canza ranakun haihuwa da ɗalibai keyi

- Mai kula da kuma ajiye muhimman bayanai a hukumar, Prof. Is-haq Oloyede ne ya bayyana haka a babban birnin tarayya, Abuja

- Ya ce dayawan mutane na miƙa bukatar canza ranar haihuwarsu ne saboda su cika sharuɗɗan (NYSC)

Hukumar dake shirya jarabawar share fagen shiga jami'a a Najeriya (JAMB) tace ta tara kuɗaɗe da suka kai 400 miliyan saboda yawan canza ranar haihuwa da ɗalibai keyi.

Mai kula da aje bayanan ɗalibai na hukumar, Prof. Is-haq Oloyede, ya ce a shekararsa ta farko a wannan ofishin ya tara waɗannan kuɗaɗen masu yawa.

KARANTA ANAN: An yanka ta tashi: ‘Yan Sanda sun cafke ‘Yan OPC da su ka kama 'Shugaban 'Yan bindiga'

Ya ƙara da cewa mutane dayawa na ziyartar shafin hukumar don canza ranar haihuwarsu ba don komai ba sai don su sami damar zuwa hidimar ƙasa (NYSC).

Shugaban ya yi wannan jawabi ne yayin wani taron ƙara wa juna sani da (NYSC) ta shiryawa makarantun gaba da sakandire da kuma wasu masu ruwa da tsaki a Abuja.

A shekara ɗaya, Mun tara 400 miliyan saboda canza ranar haihuwa, Oloyede
A shekara ɗaya, Mun tara 400 miliyan saboda canza ranar haihuwa, Oloyede Hoto: @JAMBHQ
Asali: Twitter

Oloyede yace shi kaɗai keda hurumin canza ranar haihuwa a hukumar, bayan mutum ya cike wasu sharuɗɗa.

Ya ce: "A shekarata ta farko a matsayin mai kula da kuma ajiye muhimman bayanai (regitrar), mun samu kuɗaɗe 400 miliyan daga masu buƙatar canza ranar haihuwarsu."

"Nayi mamaki matuka da gaske akan meyasa mutane keson canza ranakun haihuwarsu, ba don muna son tara kuɗi bane mukasa waɗannan dokokin na biyan kuɗi." a cewarsa.

KARANTA ANAN: An yankewa wasu 'yan Nigeria biyu hukuncin kisa a Ghana

Ya kuma cigaba da cewa: "Idan kanason canza wani abu dole ka faɗi mana dalili. Idan ka tambayi wanda ke bautar ƙasa a yanzu, zai faɗa maka dalilan dayasa (JAMB) ke ƙin amincewa shine saboda (NYSC)"

Oloyade ya ƙara da cewa: "Dayawa suna son rage shekarunsu ne saboda su cika sharuɗɗan (NYSC). Kuma kafin kowanne canza shekaru ya fara aiki sai yazo gaba na, ni kaɗai keda alhakin hakan."

"Babu wanda zai amince da canza ranar haihuwa a hukunar (JAMB) sai ni kaɗai, ni kaɗai keda lambobin sirrin da za'a amince da hakan," inji Oloyede.

A wani labarin kuma Jami'an yan sanda sun cafke 'Yan OPC da suka kama 'Shugaban 'Yan bindiga'

'Yan sandan na zargin wadannan mutane da yin kisan-kai a wajen kama wannan mutumi

Ana zargin Iskilu Wakiliin Ayete shi ne shugaban ‘yan bindigan da su ke ta’adi a Ibarapa, jihar Oyo.

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwanan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel