An yankewa wasu 'yan Nigeria biyu hukuncin kisa a Ghana

An yankewa wasu 'yan Nigeria biyu hukuncin kisa a Ghana

-Wata babbar kotu a Sekondi dake kasar Ghana ta yankewa wasu 'yan Najeriya biyu, Samuel Udoetuk Wills da kuma John Orji hukuncin kisa bayan kamasu da laifin da tayi

-Kotun ta kama 'yan Najeriyan ne da laifin sace mata hudu da kuma kashe su

-Hukuncin ya ɗauki tsawon shekaru biyu ba'a ƙarƙareshi ba, domin tun shekarar 2018 aka kama su

Wata babbar kotu dake garin Sekondi na ƙasar Ghana ta yanke wa wasu 'yan Najeriya biyu hukuncin kisa.

Hukuncin ya biyo bayan tabbatar da laifin su na sace wasu mata huɗu da kuma kashe su.

Kotun ta yanke ma Samuel Udoetuk Wills, da kuma John Orji hukuncin ne a jiya bayan tabbatar da sun aikata laifin da wasu shaidu bakwai sukayi.

KARANTA ANAN: Rikicin Siyasa: Gwamnan Edo ya bayyana babban abinda ke haɗa shi da Adams Oshiomhole

The Nation ta ruwaito cewa an ɗau dogon loƙaci da yakai shekaru biyu ana shari'ar.

Alƙalin kotun yace, waɗan da ake zargi na da damar ƙalubalantar hukuncin a cikin kwanaki 30.

An kama 'yan Najeriyan ne bisa zargin sace wa da kuma kashe wasu mata har guda huɗu.

An yankewa wasu 'yan Nigeria biyu hukuncin kisa a Ghana
An yankewa wasu 'yan Nigeria biyu hukuncin kisa a Ghana Hoto: thenationonlineng.net
Source: UGC

An bayyana cewa anga matan ne tsakanin watan yuli da disamba a wurare daban-daban da suka haɗa da Kansawurodo, Butumagyebu, Nkroful junction kafin daga bisani a neme su a rasa.

KARANTA ANAN: Gwamnati ta yi watsi da jita-jitar cewa zata kashe 10 biliyan wajen rarraba rigakafin corona

Bayan watanni da 'yan uwansu suka ɗauka suna neman su basu gansu ba, mutanen garin sunyi zanga-zangar neman abi musu haƙƙinsu wajen nemo su.

Daga karshe hukumar 'yan sanda sun gano wasu ƙasusuwa a gidan waɗanda ake zarigi, kuma bayan gwaje-gwaje a asibiti aka tabbatar ragowar ƙasusuwan Matan ne.

Bayan haka, 'yan sanda sun tsananta bincike inda daga karshe suka gano waɗan da ake zargin kuma suka miƙa su ga shari'a.

A wani labarin kuma Zulum ya dira sansanin 'yan gudun hijira cikin dare, ya gano 'yan gudun hijiran bogi

Gwamnan ya tabbatar da kame 'yan gudun hijra na bogi sama da 600 dake wawashe abinci

Gwamnan kai ziyara sansanin ne da tsakar dare domin gane wa idonsa abubuwan da ke faruwa

Ahmad yusuf sabon ma'aikaci ne a legit.ng daya fara aiki kwanan nan. Ahmad nada burin zama babban ɗan jarida.

Zaku iya bibiyar Ahmad a shafinsa na twitter @ahmadyusufmuha77

Source: Legit.ng

Online view pixel