Gwamnan Ekiti ya kai ziyara ga iyalan manoman da makiyaya suka kashe

Gwamnan Ekiti ya kai ziyara ga iyalan manoman da makiyaya suka kashe

- Gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi ya kai ziyara ta musamman ga iyalan manoman da wasu mutane da ake zargin makiyaya ne suka kashe

- Kisan manoman da akayi a yankin Isaba karamar hukunar Ikole, Jihar Ekiti ya jawo tashe-tashen hankula

- A lokacin da gwamnan yakai ziyarar da safen nan ya yi alƙawarin cewa za'a kamo duk wani mai hannu a kisan

Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya kai ziyara ga iyalan wasu manoman jihar da aka kashe ranar Juma'a.

Ana zargin fulani makiyaya da aikata lamarin kamar yadda jaridar Punch ta wallafa.

KARANTA ANAN: Yawan kabilu da addinai ke jawo kalubale wajen gina Najeriya, Osinbajo

Kisan ya fusata mazauna garin Isaba, a karamar hukumar Ikole, jihar Ekiti, hakan yasa suka yi zanga-zangar da ta jawo asarar wasu abubuwan hawa da wuraren kasuwanci.

Gwamnan ya yi alƙawarin kamo waɗanda suka aikata wannan aika-aika domin su fuskanci hukunci daidai da abinda suka aikata.

Gwamnan Etiki ya kai ziyara ga iyalan manoman da makiyaya suka kashe
Gwamnan Etiki ya kai ziyara ga iyalan manoman da makiyaya suka kashe Hoto @kfayemi
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Rikicin Siyasa: Gwamnan Edo ya bayyana babban abinda ke haɗa shi da Adams Oshiomhole

Ya rubuta a shafinsa na twitter: "A jiya aka tsinci gawarwakin biyu daga cikin manoman mu daga yankin Isaba, Mr Toyin Akeju wanda akafi sani da Jisoro da kuma Mr Yusuf Onuche, wanda aka gansu da alamar harbi a jikinsu."

"Ana zargin makiyayan Bororo da kashe su har lahira," a cewar gwamnan.

"Na ziyarci iyalan da abun ya shafa yau da safe domin tabbatar musu gwamanti na bayan su Kuma zamuyi iya iyawarmu wajen kamo duk waɗanda keda hannu a faruwar lamarin," inji Fayemi.

Gwamnan ya kara da cewa wannan kashe-kashen yayi yawa kuma gwamnati zatayi iya iyawarta don kare rayuwakan yan jihar.

A wani labarin kuma Gumsu Abacha ta yi wuf da Gwamna Mai Mala Buni, Maryam Abacha ta shiga farin ciki

Diyar Sani Abacha, Gumsu Abacha ta auri Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni. An yi bikin auren ne a gidan Mohammed Abacha a babban birnin tarayya, Abuja

Yanzu haka ita ce mata ta hudu ga Gwamna Buni, wanda ya auri diyar wanda ya gada, Ummi Adama Gaidam a kwanakn baya.

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwanan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd

Asali: Legit.ng

Online view pixel