Fani-Kayode ga Gumi: Kada ka saka Najeriya cikin rikici mai wuyar karewa da tsokacinka

Fani-Kayode ga Gumi: Kada ka saka Najeriya cikin rikici mai wuyar karewa da tsokacinka

- Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya zargi Gumi da yunkurin jefe Najeriya cikin rikici

- Fani-Kayode yace bashi da tabbaci idan malamin bai zama mai magana da yawun 'yan ta'adda masu kashe-kashe da garkuwa da mutane ba

- Jigon jam'iyyar PDP yace akwai bukatar a duba lafiyar Malamin ta yadda yake ta tsokacin da ke baiwa 'yan ta'adda kariya

Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya caccaki fitaccen malamin addini, Sheikh Ahamd Gumi a kan tsokacinsa, inda yace a ninke yake a cikin duhu.

Fani-Kayode yayi martani ne a kan tsokacin Gumi inda yace in har za a iya yafewa masu shirya juyin mulki, me zai sa ba za a iya yafewa 'yan binidga ba?

Fani-Kayode yace "Ta yuwu mu yiwa Hitler, Pol Pot, Stalin, King Leopard 11 na Belgium, Osama Bin Ladin, Al Bagdadi, Abubakar Shekau da duk wani wanda ya kashe mutane da yawa afuwa bayan mutuwarsu saboda tarihin da suka kafa a duniya.

"A farko ya bukaci 'yan ta'addan da su mayar da hankali wurin harar sojoji kiristoci, daga baya yace satar yaran makaranta karamin laifi ne, yanzu kuma ya sauya salo.

KU KARANTA: Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana babban sirrinsa na haddar Al-Qur'ani

Fani-Kayode ga Gumi: Kada ka saka Najeriya cikin rikici mai wuyar karewa da tsokacinka
Fani-Kayode ga Gumi: Kada ka saka Najeriya cikin rikici mai wuyar karewa da tsokacinka. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

“Ko dai Sheikh Ahmad Gumi ya rasa hankalinsa ne. Ko yana bukatar tallafin gaggawa na likitoci. Ko kuma ya zama mai magana da yawun 'yan ta'addan da ke yankan rago, azabtarwa, fyade da garkuwa da mutane a kasar nan?"

Fani-Kayode yace ya sakankance Gumi baya cikin hayyacinsa kuma akwai wani abu da yake ba daidai ba da malamin.

"A ninke yake cikin duhu da yaudara. Wani ya sanar dashi cewa mun ji kalamansa masu kama da surkulle, hatsari da rashin kan gado.

"Kasar nan a halin yanzu tana dab da shiga cikin rikici. Kada Gumi ya hankada mu cikin rikici da tsokacinsa masu bada takaici da rashin ma'ana," ya kara da cewa.

KU KARANTA: Nan babu dadewa zaka dawo jam'iyyar APC, Zulum ga Gwamnan Bauchi

A wani labari na daban, wasu mutane da aka tsare sakamakon zarginsu da ake yi da zama 'yan Boko Haram sun bukaci wata babbar kotun tarayya da ke zama a Legas da ta kwatar musu hakkinsu na tsaresu tsawon shekaru 12 da aka yi ba tare da an yi musu hukunci ba.

Ta hannun lauyansu Ahmed Adetola-Kazeem na kungiyar kare hakkin 'yan fursuna, suna bukatar kotu ta bada umarnin sakinsu da gaggawa.

Sun kara da mika bukatar a dakatar da wadanda ke zarginsu daga sake take musu hakkinsu na dan Adam a kowacce hanya, The Nation ta ruwaito.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel