Da duminsa: Dakarun soji sun fatattaki 'yan Boko Haram daga Borno
- Zakakuran sojin Najeriya sun fatattaki 'yan Boko Haram da suka kai samame hanyar damaturu zuwa Maiduguri
- Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da safe bayan sojoji sun bude hanyar Damaturu da ake rufewa a kowanne yammaci
- Wani direba ya tabbatar da cewa dakarun sojin da mayakan ta'addancin sun yi musayar ruwan wuta a Mainok da Jakana
A ranar Lahadi ne sojojin Najeriya suka hana mayakan Boko Haram daga mamaye babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri a jihar Borno.
An gano cewa sojojin sun yi musayar wuta tsakaninsu da 'yan Boko Haram a garin Mainok da Jakana.
Wani matukin motar haya ya sanar da Daily Trust cewa lamarin ya faru ne jim kadan bayan an bude titin da aka saba rufewa duk yammaci.
Sojojin suna rufe babbar hanyar duk yammaci kuma su budeta da karfe 7 na safiyar kowacce rana.
KU KARANTA: Ina da tabbacin Buhari ba bacci yake ba, Jonathan a kan rashin tsaron Najeriya
Direban yace wasu 'yan Boko Haram sun yi kokarin mamaye titin tare da kaiwa matafiya hari amma sojojin sun fatattakesu.
"Muna kan hanyarmu ta zuwa Maiduguri inda muka kwana a Damaturu bayan sojoji sun tare mu a wani wuri gaba da Mainok.
“Tun farko an bukaci mu juya amma daga baya sai aka bukaci mu tsaya. Daga baya mun fara jin harbe-harbe. Bayan minyuna 30 sai aka ce zamu iya tafiya," yace.
Yace a halin yanzu an zuba sojoji somin sintiri a hanyar.
KU KARANTA: Kamar El-Rufai, gwamnan Kogi yace ba zai yi sasanci da 'yan ta'adda ba
A wani labari na daban, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya caccaki fitaccen malamin addini, Sheikh Ahamd Gumi a kan tsokacinsa, inda yace a ninke yake a cikin duhu.
Fani-Kayode yayi martani ne a kan tsokacin Gumi inda yace in har za a iya yafewa masu shirya juyin mulki, me zai sa ba za a iya yafewa 'yan binidga ba?
Fani-Kayode yace "Ta yuwu mu yiwa Hitler, Pol Pot, Stalin, King Leopard 11 na Belgium, Osama Bin Ladin, Al Bagdadi, Abubakar Shekau da duk wani wanda ya kashe mutane da yawa afuwa bayan mutuwarsu saboda tarihin da suka kafa a duniya."
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng