Zulum ya dira sansanin 'yan gudun hijira cikin dare, ya gano 'yan gudun hijiran bogi

Zulum ya dira sansanin 'yan gudun hijira cikin dare, ya gano 'yan gudun hijiran bogi

- Gwamnan jihar Borno ya dira sansanin gudun hijira domin tantance na gaskiya da na karya

- Gwamnan ya tabbatar da kame 'yan gudun hijra na bogi sama da 600 dake wawashe abinci

- Gwamnan kai ziyara sansanin ne da tsakar dare domin gane wa idonsa abubuwan da ke faruwa

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umaru Zulum ya yi wa wani sansanin 'yan gudun hijira dirar ba-zata inda ya gano daruruwan 'yan gudun hijira na bogi.

Sanarwar da gwamnatin Borno ta aike wa BBC ta ce daga cikin 'yan gudun hijira 1,000 da ke cikin kundin jami’an agaji a yankin, 650 daga cikinsu na bogi ne.

KU KARANTA: Fadar Shugaban Kasa: Buhari bai jikkata ba bayan yin rigakafin Korona

Zulum ya dira sansanin 'yan gudun hijira cikin dare, ya gano 'yan gudun hijiran bogi
Zulum ya dira sansanin 'yan gudun hijira cikin dare, ya gano 'yan gudun hijiran bogi Hoto: @GovBorno
Asali: Twitter

Sanarwar ta ce gwamnan ya kai ziyara ne a sansanin kwalejin Mohammed Goni MOGOCOLIS inda ake kula da mutanen karamar hukumar Abadam a arewacin Borno da rikici ya rabasu da gidajensu.

“Gwamna Zulum ya yi shigar ba-zata ne sansanin 'yan gudun hijirar da tsakiyar dare tare da rufe sansanin domin tantance yawan ƴan gudun hijirar,” in ji sanarwar.

Zulum ya dira sansanin 'yan gudun hijira cikin dare, ya gano 'yan gudun hijiran bogi
Zulum ya dira sansanin 'yan gudun hijira cikin dare, ya gano 'yan gudun hijiran bogi Hoto: @GovBorno
Asali: Twitter

Sannan ta ce gwamnan ya yi hakan ne domin gano masu karyar cewa 'yan gudun hijira ne da ke shafe kwanaki a sansanin suna karbar abincin da aka tanadar wa 'yan gudun hijira, kuma idan dare ya yi su tafi gidajensu.

Zulum ya dira sansanin 'yan gudun hijira cikin dare, ya gano 'yan gudun hijiran bogi
Zulum ya dira sansanin 'yan gudun hijira cikin dare, ya gano 'yan gudun hijiran bogi Hoto: @GovBorno
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamnati bata isa ta hana kiwo a fili ba, in ji Miyetti Allah Kautal Houre

A wani labarin, ‘Yan mata 317 da aka sace daga Makarantar Sakandaren ’Yan mata ta gwamnati, da ke Jangebe, a Jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Nijeriya, sun dawo, in ji Gwamnan Jihar.

Gwamna Matawalle ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita cikin daren Talata, 2 ga Maris, 2021. A jawabinsa, ya bayyana irin jajircewan da suka yi domin ganin cewa an sako wadannan dalibai 317.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel