Gwamnati bata isa ta hana kiwo a fili ba, in ji Miyetti Allah Kautal Houre

Gwamnati bata isa ta hana kiwo a fili ba, in ji Miyetti Allah Kautal Houre

- Kungiyar Miyetti Allah Kautal Houre ta yi Allah wadai da kudurin hana makiyaya kiwo a fili

- Kungiyar ta saba da takwararta da ta amince da dokar hana kiwon a wasu yankunan kudanci

- Hakazalika kungiyar ta yi alwashin cewa gwamnati bata isa ta hana makiyaya kiwo a fili ba

Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah Kautal Houre, ta ce tana adawa da dokar hana kiwo a fili da gwamnonin Kudu maso Yamma suka sanya. Sanarwar ta ce aiwatar da dokar daidai take da sanarwar korar mutane.

Wannan ya sabawa matsayin kungiyar Makiyaya na Najeriya ta Miyetti Allah, wacce a wata ganawa da wasu gwamnoni a Akure, babban birnin jihar Ondo, a ranar 25 ga watan Janairu, ta ce ta amince da matsayin gwamnonin.

Shugaban kungiyar, Alhaji Muhammadu Kiruwa ne ya jagoranci kungiyar ta Miyetti Allah zuwa taron, tare da sauran mahalarta taron.

Baya ga gwamnonin Kudu maso Yamma, gwamnonin yankin Kudu maso Gabas a baya sun hana yin kiwo a fili da kuma shigar da shanu a kafa zuwa yankin Kudu maso Gabas.

KU KARANTA: Labari mara dadi: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mutune 11 a jihar Kaduna

Gwamnati bata isa ta hana kiwo a fili ba, in ji Miyetti Allah Kautal Houre
Gwamnati bata isa ta hana kiwo a fili ba, in ji Miyetti Allah Kautal Houre Hoto: The Punch
Asali: UGC

Amma a wata hira da jaridar Punch ta ranar Asabar, Sakatare Janar na Miyetti Allah Kautal Houre, Saleh Alhassan, ya ce a ranar Juma’a,

“Ba za su iya kawo karshen makiyaya kai tsaye ba saboda kiwo ba sana’ar babur ba ce; dole ne a samu wani madadi. Abu na biyu, idan suka ce zasu kawo karshen kiwo a fili, menene jadawalin shi?

“Suna son korar makiyaya daga inda suke samun kudin shiga ne. Bai bambanta da sanarwar kora ba - kawai yana sanya sanarwar korar ne a aikace.

"Wannan abin takaici ne matuka saboda ba za su iya fitowa su ce suna rungumar makiyaya cikin lumana ba sannan kuma suna cewa suna son kawo karshen kiwo a fili. Me suke nufi da hakan? Shin akwai kiwo a rufe ne?

“Daga tarihi, tun zamanin annabi Musa, ana kiwo a fili. Zuwa yanzu, ya kamata su gane cewa ba za su sami sakamakon da suke nema ba.

"Muna da cikakken goyon baya ga Tsarin Canjin Tsarin Dabbobin Kasa. Ina daga cikin kwamitin da ya duba takaddar karshe. Shirin yana da abubuwa da yawa, kuma idan aka aiwatar dashi, zai magance kalubale da yawa.

“Dubi jihar Benue da yadda dokar ta haifar da fitina. Ba za ku iya kawo karshen kiwo a fili ta hanyar kai tsaye ba kamar ana neman rikici, kuma wadannan rikice-rikicen suna da hanyar da za su sake tattaunawa.”

Alhassan ya yi ikirarin cewa doka kan makiyaya su daina kiwo a fili kuma su fara kiwo a kebe daidai yake da neman manoma su fara noman zamani na inji, wanda ba tare da su ba ba za su iya gudanar da ayyukansu na noma ba.

KU KARANTA: Hayakin Janareta ya yi sanadiyyar mutuwar wasu daliban jami'a 2

A wani labarin, Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo a ranar Laraba ya nanata cewa jihar ba za ta bayar da filaye kyauta don kiwo ba, yana mai cewa kiwo kasuwanci ne na kashin kai, Channels Tv ta ruwaito.

Gwamnan ya fadi hakan ne a cikin wasu sakonni da ya wallafa a shafin sa na Twitter yayin da yake karin bayani kan wani bayani da ya gabatar a baya game da shirin sauya fasalin kiwon dabbobi a yayin taron tsaro da aka gudanar a ranar Litinin.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel