Wata sabuwa: WAEC ta soke jarabawar ɗalibai masu zaman kansu

Wata sabuwa: WAEC ta soke jarabawar ɗalibai masu zaman kansu

- Hukumar dake shirya jarabawar WAEC a Najeriya ta soke jarawar da ɗalibai masu zaman kansu suka yi

- Hukumar ta sake sanya ranar da ɗaliban zasu sake yin jarabawar

- Ta kuma bayyana matakan da makarantun gwamnati zasu bi don su biya kudin jarabawar ta wannan shekarar

Hukumar dake shirya jarabawar fita ɗaga sakandire (WAEC) tace ta soke jarabawar "Litrature-in-English" da ɗalibai masu zaman kansu sukayi.

Sai dai zuwa yanzun basu bayyana dalilin soke jarabawar ba kamar yadda jaridar Thenation ta wallafa.

KARANTA ANAN: Makaho da iya shege: An yi ram da wani mara gani da yake damfarar Bayin Allah

Ɗaliban sunyi jarabawar ne a ranar 26 ga watan Fabrairu.

Hukumar tace za'a sake yin jarabawar a ranar 10 ga watan maris.

Wata sabuwa: WAEC ta soke jarabawar ɗalibai masu zaman kansu
Hoto: @waecnigeria
Wata sabuwa: WAEC ta soke jarabawar ɗalibai masu zaman kansu
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: NAFDAC ta amince ayi amfani da rigakafin Astrazeneca a Najeriya

An fara jarabawar (WAEC) ɗin ne ta ɗalibai masu zaman kansu a ranar 15 ga watan fabrairu.

Bayan haka, WAEC ta fitar da sabbin matakan da za'a bi don yin rijistar jarabawar ga ɗaliban makarantun gwamnati.

Hukumar ta ce, kowacce makaranta sai ta biya N13,950 a ɗaya daga cikin bankunan da suka amince da su.

A wani labarin kuma Sheikh Gumi ya hakikance a kan yi wa ‘Yan bindiga afuwa duk da matsayar Gwamnatin Buhari

Shehin Malamin ya na ganin babu wani dalilin kin yi wa ‘Yan bindiga lamuni

Dr. Gumi ya ce an yi lokacin da aka yafewa wadanda su ka kifar da Gwamnati

Ahmad Yusuf dan mtan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: