Makaho da iya shege: An yi ram da wani mara gani da yake damfarar Bayin Allah
- An kama wani Makaho mai suna Tochukwu Ikebuife mai damfarar mutane
- Ana tuhumar wannan mutumi da damfarar ‘yan mata da samari a Anambra
- Tochukwu Ikebuife da matarsa, Nkiru, sun shiga ragar jami’an tsaro a yanzu
Wani mutum maras ido da yake damfarar mutane ya shiga hannun rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Anambra.
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa an kama Mista Tochukwu Ikebuife wanda aka fi sani da “Mmanye” da laifin damfarar Bayin Allah.
Tochukwu Ikebuife ya kan tofa yawu a tafin hannun mutane, sai yawunsa ya fito a bayan hannuwansu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa har da mai dakin wannan ‘dan damfara, Nkiru Ikebuife aka kama, duk su na tsare a hannun jami'an tsaro.
KU KARANTA: Boko Haram: Ana cigiyar Sojojin da su ka ci kafar kare a Borno
Kananan yara da ‘yan mata musamman wadanda su ke tsaron shago ko koyon aiki a kasuwannin Onisha su ka fi fada wa hannun Ikebuife.
Dakarun ‘yan sanda a karkashin jagorancin SP Noel Uche ne su ka cafke Ikebuife a garin Obosi, karamar hukumar Idemili ta Arewa da ke jihar Anamba.
Tochukwu Ikebuife, ainihinsa mutumin garin Ire ne a yankin Obosi, Ana zarginsa da karbar kudi daga N500, 000 har zuwa Naira miliyan 5 ta hanyar damfara.
Da ya kai wa SP Noel Uche ziyara a garin Ukwu, shugaban kungiyar Ndigbo Unity Forum, Uzor A. Uzor ya sanar da cewa an kama makahon da uwargidarsa.
KU KARANTA: An yi fatali da rokon EFCC na karbe gidan Saraki a Legas
Kungiyar Ndigbo Unity Forum ta dauki mutane bakwai da wannan mutumi ya damfara zuwa wajen ‘yan sanda, ta yi kira ga jami’an tsaro su gurfanar da shi.
“Jama’a su yi hattara da irin wadannan mutane. Wannan na cikin dabarunsu. Ina kiran ‘yan sanda su yi maza su maka wanda ake zargi da matarsa a kotu.”
Dazu kun ji Ahmad Abubakar Gumi ya na nan a kan bakarsa, ya dage a kan cewa ya kamata gwamnatin tarayya ta yafe wa 'yan bindiga domin sun ce sun tuba.
Dr. Ahmad Gumi ya ke cewa duk da an taba yafe wa wadanda su ka kifar da Gwamnati a Najeriya da wadanda jawo yakin Biyafara, 'yan bindiga sun cancani afuwa.
Shehin ya yi wa CAN raddi, ya ce ya na ganin babu wani dalilin kin yi wa ‘Yan bindiga lamuni.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng