Sheikh Gumi ya hakikance a kan yi wa ‘Yan bindiga afuwa duk da matsayar Gwamnatin Buhari
- Sheikh Ahmad Gumi bai sauya ra’ayi ba a kan yafe wa Miyagun ‘Yan bindiga
- Shehin Malamin ya na ganin babu wani dalilin kin yi wa ‘Yan bindiga lamuni
- Dr. Gumi ya ce an yi lokacin da aka yafewa wadanda su ka kifar da Gwamnati
Shahararren malamin addinin musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya dage a kan bakarsa na yi wa ‘yan bindiga afuwa.
Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya ce idan za a iya yi wa wadanda su ka kifar da gwamnati afuwa, babu laifi don a yafe wa ‘yan bindiga.
Jaridar Punch ta rahoto malamin ya na wannan magana ne a ranar Alhamis, 4 ga watan Maris, 2021.
Shehin ya maida martani ne ga kungiyar Kiristocin Najeriya watau CAN a garin Kaduna. Ahmad Gumi ya ce akwai bukatar ayi afuwa saboda a zauna lafiya.
KU KARANTA: Abin da ya sa muke neman ayi sulhu da ‘yan bindiga -IGP
“Har wadanda su ka haddasa yakin basasa, yakin da ya ci miliyoyin mutane, an yade masu. Ban ga dalilin da ba za mu amince da tuban ‘yan bindiga ba.”
Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya ce ya kamata gwamnati ta yi lamuni, ta yafe wa miyagun.
Babban malamin ya yi karin-haske game da wasu kalamai da aka ji ya yi, yake cewa kungiyar CAN ba ta fahimce shi ba ne, saboda an rikidar da maganarsa.
“Ku na tambaya meyasa mu ke neman ayi masu lamuni? Sun fada mana cewa sun shirya ajiye makamai, amma ba su son a bi su da kara a kotu bayan sun tuba.”
KU KARANTA: Yin sulhu da 'yan bindiga hatsari ne - HURIWA
Ya ce: “Idan kasar nan za ta iya yin afuwa ga wadanda su ka ci amana a lokacin mulkin soja, za a iya yi wa ‘yan bindiga afuwar da ta fi wannan a mulkin farar hula.”
Kwanaki Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi magana game da matsalar ‘yan bindiga. Ya ce Ahmad Gumi abokinsa ne, amma ba ya tare da shi kan batun sulhu.
Kafin ya bar ofis, Janar TY Buratai ya bayyana cewa matsayar rundunar soji ita ce babu sulhu da 'yan bindiga.
Kwanan nan ne Garba Shehu ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya ba hukumomin tsaro umurnin bindige duk wanda su ka kama dauke da bindigar AK-47.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng