'Yan majalisar jam'iyyar APC biyu sun koma PDP a Bauchi

'Yan majalisar jam'iyyar APC biyu sun koma PDP a Bauchi

- 'Yan majalisun dokoki na jihar Bauchi guda biyu sun fice daga APC sun koma PDP

- 'Yan majalisar da suka koma jam'iyyar ta PDP sune Yusuf Bako da Umar Yakubu

- Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Abubakar Suleiman ne ya karanto wasikun sauya shekar a zaman majalisar na ranar Laraba

'Yan majalisar dokokin jihar Bauchi guda biyu sun fice daga jam'iyyar All Progressives Congress, APC, sun koma Peoples Democratic Party, PDP a jihar, rahoton The Punch.

Mai magana da yawun kakakin majalisar dokokin jihar ta Bauchi, Abdul Burra ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar a ranar Laraba kuma ya raba wa manema labarai sanarwar.

'Yan majalisar jam'iyyar APC biyu sun koma PDP a Bauchi
'Yan majalisar jam'iyyar APC biyu sun koma PDP a Bauchi. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Mambobin majalisar sune Yusuf Bako mai wakiltar mazabar Pali da Umar Yakubu mai wakiltar mazabar Udubo.

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa ango rasuwa kwana ɗaya bayan ɗaurin aurensa

Ya ce yan majalisar sun sanar da ficewarsu daga APC ne cikin wata wasika da kakakin majalisar, Abubakar Suleiman ya karanto yayin zaman majalisar.

Ya ce Yakubu, a wasikarsa ya ce ya fice daga APC ne daga ranar 2 ga watan Maris na 2021.

"Ya yi alkawarin cigaba da bada gudunmawa don kare hakkin al'ummarsa da cimma manufofin gwamnatin Bauchi mai ci a yanzu."

Burra ya kara da cewa kakakin majalisar ya kuma karanto wasikar Bako inda ya ce sanar da majalisar cewa ya fice daga APC ya koma PDP.

KU KARANTA: Abdul-Jabbar: JNI ta ce ba za ta hallarci muqalabar da gwamnatin Kano ta shirya ba

Bako ya ce ya tuntubi jama'ar mazabarsa inda suka bukaci ya koma PDP domin ganin gwamnatin da ke ci ta cigaba da samun nasara saboda irin ayyukan cigaba da ta ke yi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa a halin yanzu, PDP tana da yan majalisa 11 yayin da PC na da 19 a majalisar dokokin ta jihar Bauchi.

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta kama wani mai fataucin miyagun kwayoyi mai shekaru 36 dauke da hodar Iblis da ta kai na Naira biliyan daya.

NDLEA ta ce mai safarar, Nkem Timothy, wanda ya yi basaja a matsayin Auwalu Audu domin yin fataucin kunshin hodar Iblis da nauyinsa ya kai 1.550kg. An yi kiyashin kudinsa ya kai Naira biliyan 1.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da ya ke kokarin zuwa Algeria ta bodar jamhuriyar Nijar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel