Yin sulhu da 'yan bindiga yana da hatsari, in ji HURIWA

Yin sulhu da 'yan bindiga yana da hatsari, in ji HURIWA

- Kungiyar marubuta ta HURIWA ta gargadi gwamnatin tarayyar Nigeria game da sulhu da yan bindiga

- Shugaban kungiyar na kasa, Emmanuel Onwubiko ne ya yi wannan gargadin a ranar Litinin a Abuja yayin zantawa da manema labarai

- HURIWA ta ce sulhu da wadanda ke barazana da tsaron kasa kuskure ne ya saba da dokar yaki da ta'addanci da ke kundin tsarin mulki

Kungiyar Marabuta Masu Kare Hakkin BIldama (HURIWA) ta gargadi gwamnatin tarayya kan matsalolin da ka iya bullowa sakamakon yin sulhu da yan bindiga.

Kungiyar ta ce bai kamata gwamnati ta rika sulhu da wanda ke barazana ga tsaron kasa ba, The Nation ta ruwaito.

Yin sulhu da 'yan bindiga yana da hatsari, in ji HURIWA
Yin sulhu da 'yan bindiga yana da hatsari, in ji HURIWA. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Mun sha duka da yunwa: Fasinjojin da ƴan bindiga suka sace a Neja sun magantu

Shugaban kungiyar na kasa, Emmanuel Onwubiko ne ya yi wannan jawabin ranar Litinin a Abuja yayin zantawa da manema labarai.

HURIWA kuma tana duba yiwuwar karar Shugaba Muhammadu Buhari da Majalisar Tarayya don tilasta musu amfani da dokar yaki da ta'addanci idan har manya a gwamnatin tarayya suka cigaba da kusantar yan ta'adda da yan bindiga wanda hakan ya sabawa dokar yaki da ta'addanci.

KU KARANTA: Matar aure na neman saki saboda mijinta ya 'kasa yi mata ciki'

Ta ce matakin da Shugaba Buhari ya dauka na amincewa da tattaunawa da yan bindiga kamar yadda Malamin Kaduna Sheikh Ahmad Gumi ke jagoranta, "cin amanar kasa ne kuma ya saba wa dokar yaki da ta'addanci da ke kundin tsarin mulkin Nigeria."

Kungiyar ta kuma nuna damuwar ta kan kalaman da Gumi ya yi amfani da su inda ta ce, "Idan da gaske malamin addinin musuluncin ya dora wa sojoji kirista laifi kan kashe yan bindiga, toh, wannan cin amanar kasar ma ta baci, idan har ta tabbata ya fada."

A wani labarin daban, basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.

Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel