Abinda ya sa muke neman sulhu da ‘yan bindiga, inji Sufeto janar na ‘yan sanda

Abinda ya sa muke neman sulhu da ‘yan bindiga, inji Sufeto janar na ‘yan sanda

Sufeto janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu yayi magana a kan batun yin sulhu tsakanin jami’an ‘yan sanda, ‘yan bindiga da kuma kuma gwamnonin jihohin arewacin Najeriya inda ya ce abu ne mai kyau wanda zai kawo zaman lafiya.

Adamu ya ce an samu saukin ayyukan ‘yan bindiga da kuma masu garkuwa idan aka yi la’akari da yadda abubuwan ke aukuwa a watannin baya.

KU KARANTA:Ba abinda Buhari ya yiwa Najeriya banda jefata cikin halin kunci da talauci – Sheikh Gumi

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala tattaunawar shugabannin hukumomin tsaro da Shugaba Buhari, Adamu ya ce marigayi Shugaba Umaru Yar’Adua yayi amfani da irin wannan hanya ta sulhu domin magance matsalar ‘yan Neja-Delta.

Adamu ya ce: “Idan muna maganar samar da zaman lafiya akwai abubuwa daban-daban da akeyi, ba lallai bane hakan na nufin sai ka bada wani abu kafin samun biyan bukatarka. Maganar sulhu kuwa ba a arewacin Najeriya aka soma yinta ba a kasar nan.

“Idan baku manta ba a shekarun baya mun kasance muna samun matsaloli da ‘yan yankin Neja-Delta. A wancan lokacin da gwamnati ta tsaya tayi nazarin cewa ba yaki bane zai magance matsalar sai ta nemi sulhu.

“A don haka a gani na dubarun yaki ba lallai sai an dauki makami ba, akwai hanyar neman sulhu wadda a lokuta da dama tafi samr da zaman lafiya nan take. Bai zama wajibi a ce domin mutum dan bindiga bane an kama shi dole sai an hukunta shi, takan yiwu ayi amfani da hanyar sulhu domin dakatar da matsalar gaba dayanta.” Inji Sufeto janar.

https://www.vanguardngr.com/2019/09/why-we-dialogue-with-bandits-igp/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel