Katsina: Buratai ya bayyana matsayin rundunar soji a kan yin sulhu da 'yan bindiga
- Laftanal Janar Tukur Buratai, ya yi watsi da shawarar 'yan siyasa a kan bukatar rundunar soji ta yi sulhu da 'yan bindiga a jihohin Katsina, Sokoto da Zamfara
- Buratai ya ce babu batun yin sulhu da 'yan bindiga tare da yin kira garesu su mika wuya, su rungumi zaman lafiya tun kafin lokaci ya kure musu
- A cewar Buratai nan da wani dan lokaci dakarun rundunar soji za su magance dukkan wasu 'yan ta'adda da su ka addabi sassan Najeriya
Babban hafsan rundunar sojojin kasa a Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya yi watsi da shawarar 'yan siyasa a kan bukatar rundunar soji ta yi sulhu da 'yan bindiga kamar yadda gwamnatocin Katsina da Zamfara suka taba yi a baya.
Buratai ya bayyana hakan ne ranar Laraba a jihar Katsina yayin da ya ke magana da manema labarai a garin Faskari mai makwabtaka da jihar Zamfara.
A cewar Buratai, rundunar soji za ta tunkari 'yan bindiga tare da kashesu matukar basu saduda sun mika wuya da kansu ba.
"Za mu tabbatar da cewa mun yaki 'yan bindiga da sauran 'yan ta'adda da ke kowanne bangare na Najeriya, amma babu batun maganar sulhu, a saboda haka na ke kira ga 'yan bindiga da sauran 'yan ta'adda a kan su mika wuya kawai, su rungumi zaman lafiya," a cewar Buratai.
Kazalika, Buratai ya yi watsi da batun zargin cewa rundunar soji ta gaza magance aiyukan ta'addanci, ya bayyana cewa rununar soji ta na iya bakin kokarinta.
DUBA WANNAN: Saurayi ya kashe budurwarsa ya jefa gawarta rijiya sboda ta ki amincewa da shi lokacin da ta ziyarci gidansa
Ya kara da cewa rundunar soji ta kashe dumbin mayakan kungiyar Boko Haram da 'yan bindiga a cikin watannin da suka gabata.
"Kwanan nan za mu gama da su," a cewar Buratai yayin da ya ke musanta zargin cewa rundunar soji ta gaza.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng