'Yan majisar jiha biyu Sun sauya sheka daga APC zuwa PDP

'Yan majisar jiha biyu Sun sauya sheka daga APC zuwa PDP

-'Yan majilisar dokoki a jihar Bauchi sun sauya sheka daga APC zuwa PDP

- Sun bayyana cewa yawan rikicin APC yasa suka guje ta

- Kakakin Majalisar ya karanta wasikun su a gaban 'yan majalisar a ranar laraba

Mambobin majalisar jihar Bauchi guda biyu sun sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar PDP.

Mai magana da yawun kakakin majalisar jihar, Abdul Burra, ya bayyana haka ga manema labarai bayan fitowa daga zaman majalisar ranar Laraba.

KARANTA ANAN: Gwamna Zulum ya fadawa Gwamnati dabaru 2 da za a bi, a kawo kashen 'Yan Boko Haram

'Yan majalisar da sukayi sauyin shekar sune: Yusuf Bako, wanda ke wakiltar mazabar Pali, da kuma Umar Yakubu, wanda ke wakiltar mazabar Udubo.

'Yan majalisun sun bayyana sauyin shekarsu ne a wata takarda da kakakin majalisar ya karanta a gaban 'yan majalisun yayin zaman su na ranar laraba.

Umar Yakubu ya bayyana a takardar da ya rubuta cewa ya bar jam'iyyar APC tun daga ranar 2 ga watan Maris.

'Yan majisar jiha biyu Sun sauya sheka daga APC zuwa PDP
'Yan majisar jiha biyu Sun sauya sheka daga APC zuwa PDP Hoto: @officialPDPNig
Source: Twitter

KARANTA ANAN: Zan yi murabus matukar hakan zai kawo karshen satar mutane, Matawalle

"A takardar da Yakubu yaturo ya bayyana dalilinsa na barin jam'iyyar APC nada alaka da yawan rikice-rikicen da ake samu a jam'iyyar." Shugaban majalisar ya bayyana.

Ya kuma kara da cewa zai cigaba da bada gudummuwa ga kudirin gwamnatin jihar na kawo cigaba ga mazauna jihar.

Burra ya kara da cewa: "Kakakin majalisar ya kuma karanta wasikar da Bako ya turo, inda ya bayyana ficewar sa daga APC."

Bako ya bayyana cewa ya yanke wannan shawarar ne bayan zaman da sukayi da al'ummar da yake wakilta.

A cewar Bako: "akwai bukatar in bayyanawa al'ummar da nike wakilta inda na dosa a siyasance, kuma in saurari ra'ayinsu."

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, yanzun jam'iyar PDP nada mutum 11 a majalisar, ita kuma APC nada 19.

A wani labarin kuma Kungiyar Ibo ta maidawa ‘Yan Arewa martani, ta ce za mu fara noma abincin da ku ke takama da shi

Kungiyar Ibon ta ce matakin nan da aka dauka zai taimakawa Kudancin kasar

Mutanen Ibo ta bakin Alex Ogbonnia sun ce noma za su fara babu kaukautawa

Ahmad Yusuf Dabai daga jihar Katsina nada burin zama cikakken dan jarida.

za'a iya tuntubarsa a shafinsa na instagram @ahmad_y_muhd

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel