2023: Wasu shugabannin APC na yiwa Bola Tinibu zagon kasa

2023: Wasu shugabannin APC na yiwa Bola Tinibu zagon kasa

- Wata kungiya ta zargi wasu daga cikin shuwagabannin jam'iyyar APC da yiwa takarar Bola Tininu zagon kasa

- Kungiyar da ta fito daga yankin kudu maso yammacin kasar nan ta goyi bayan takarar jagoran siyasar APC

- Ta bayyana Tinubu a matsayin mutum tsayayye

Wata kungiya dake kudu maso yammacin Nigeriya tayi kira ga jam'iyyar APC da ta bawa Asiwaju Bola Ahmed Tinibu takara a zabe mai zuwa.

Kungiyar dake karkashin Disciples of Jagaban, (DOJ) ta bayyana cewa akwai wasu tsiraru daga cikin shugabannin jam'iyya dake yi ma jagoran zagon kasa.

KARANTA ANAN: Allah ya yi wa ango rasuwa kwana ɗaya bayan ɗaurin aurensa

Shugaban gudanarwar kungiyar, Comrade Abdulhakeem Adegoke-Alawuje, ya fadawa manema labarai a Lagos cewa:

"Babu wani ma'aluki da zai iya dakatar da jagoran APC din."

Ya kuma bayyana Tinibu da tsayayyen dan siyasa a nigeriya.

2023: Wasu shugabannin APC na yiwa Bola Tinibu zagon kasa
2023: Wasu shugabannin APC na yiwa Bola Tinibu zagon kasa Hoto: @AsiwajuTinibu
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Daliban Jangebe sun ce da maigadin makarantarsu aka hada kai wurin sacesu

Ya kuma kara da cewa, Tinibu ne kadai tsayayyen dan siyasan da ya rage kuma ya yi aiki tukuru wajen ganin jam'iyyar APC ta amshi mulki.

Abdulkareem ya kara cewa, Tinubu ne ya kawo tsarin da ya bawa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari damar zama dan takarar APC.

Kuma hakan ya yi sanadiyyar amsar mulki da jam'iyyar tayi a zaben 2015. Karo na farko a Nigeria da Africa baki daya.

"Har zuwa yanzun bai taba korafi akan wani abu ba, ya rike girmansa na jagoran jam'iyyar kuma ya cigaba da bada shwarwawi ga gwamnatin yanzu,"

Ba tare da ya bukaci a bashi wani matsayi a gwamnati ba don ya yi mata saka masa.

A wani labarin kuma Wasu Yan Ta'adda Sun Kashe Mutum daya, sun yi awon gaba da matafiya a Osun

Wani mutum yace yaji karar harbe harbe daga kauyen su dake kusa da wajen

An tabbatar da aukuwar lamarin ranar talata da daddare

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags:
APC