Munanan hare-haren Boko Haram sun jawo Sojojin kasa fiye da 100 sun arce daga filin yaki

Munanan hare-haren Boko Haram sun jawo Sojojin kasa fiye da 100 sun arce daga filin yaki

- Ana zargin wasu sojoji da tserewa harin mayakan Boko Haram a Jihar Borno

- Sojoji kimanin 100 ne su ka bar wurin aikinsu da aka kai hari a Dikwa, Marte

- An sanar da hedikwata ana neman wadannan sojoji, za a daina ba su albashi

Rundunar sojojin kasan Najeriya ta bayyana cewa wasu jami’an ta sun bace a sakamakon harin da ‘yan Boko Haram su ka kai a Marte da Dikwa, jihar Borno.

Jaridar Daily Trust ta rahato cewa manyan jami’ai 12 da kuma sojoji 86 na dakarun ake cigiya.

A ranar Litinin, 1 ga watan Maris, 2021, aka aika takarda a hedikwatar Operation Lafiya Dole a Maiduguri, aka nuna cewa sojojin nan sun tsere ne daga aiki.

Rahoton ya ce daga cikin jami’an da ake zargin sun tsere daga yakin akwai Manjo uku, Kyaftin uku, Laftana uku, da Sajan uku, ragowar sojoji 89 duk kurata ne.

Kanal A. O. Odubiyi a madadin shugaban dakarun Operation Lafiya Dole, ya bukaci a aiko masa da bayanan wadannan sojoji da su ka tsere daga Marte da Dikwa.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sace mutane 60 , sun kona kauye a Zamfara

A. O. Odubiyi ya sanar da hedikwatar sojojin ta binciko wadannan sojoji, ta dakatar da albashinsu.

Takardar ta ke cewa: “Ana bukatar ku bayyana wadannan jami’ai da sojoji da aka ambata a matsayin wadanda su ka bar filin yaki, sannan HQ NAFC ta dakatar da biyan albashinsu, kuma a taso keyarsu zuwa hedikwatar sojoji idan aka gansu a iyakarku.”

Da aka nemi jin ta bakin mai magana da yawun bakin sojojin kasa, Birgediya-Janar Mohammed Yerima, sai ya ce gidan soja za ta yi jawabi ba tare da an tuntube su ba.

KU KARANTA: Yadda hako arzikin kasa ya yi sanadiyyar kashe-kashen da ake yi a Zamfara

Munanan hare-haren Boko Haram sun jawo Sojojin kasa fiye da 100 sun arce daga filin yaki
Sojan Najeriya Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A gidan soja, babban laifi ne jami’i ya bar inda aka ajiye shi komai runtsi. Duk wani sojan da aka samu ya aikata wannan laifi zai iya fuskantar hukunci mai tsauri.

Kwanaki kun ji yadda 'yan ta'addan kungiyar nan ta Boko Haram su ka karbe barikin Sojojin kasa da ke garin Marte, amma daga baya, sojoji sun samu sun Hkarbe kayansu.

Haka zalika kwanan nan kun ji cewa 'yan ta'addan ISWAP/Boko Haram sun kai farmaki a garin Dikwa jim kadan bayan Gwamna Babagana Zulum ya raba kayan tallafi.

Daga baya rundunar sojin Operation Lafiya Dole ta fattataki 'yan ta'addan na Boko Haram da na ISWAP wadanda suka yi yunkurin kai hari a garin Dikwa, jihar Borno.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel